Yadda haɗuwarmu ta kasance da Ganduje a filin jirgin sama : Rabi’u Kwankwaso
A karon farko, tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana yadda haɗuwarsa ta kasance da abokin takun saƙarsa na siyasa, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a filin jirgin saman Abuja, babban birnin Najeriya.
A hirar sa da BBC Hausa Sanata Kwankwaso ya shaida cewa ya riga Gwamna Ganduje zuwa filin jirgin da kamar awa guda, a lokacin ne ya samu labarin cewa shi ma magajin nasa na kan hanyar isowa filin jirgin.
“Na ce to Allah ya kawo shi, kasuwa ce ai kamar tasha ce, ba wanda za ka ce ya zo ko kar ya zo, muka shiga jirgi daya da shi muka taho, muka sauka a wanan tasha ta Kano, na kama hanyata ya kama tasa ya tafi gida.”
Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ”A matsayi irin na Musulunci ai ba lallai sai kana jam’iyya daya da mutum za ka gaisa da shi ba, mun gaisa da shi kowa ya koma ya zauna a kujerarsa, don haka haka muka isa har Kano kowa na zaune a kujerarsa.”
TUNA BAYA
Tafiya ce mai dogon tsayi, tarihin siyasar mutanen biyu ba ya cika ba tare da dayansu ba, wannan sanannen abu ne musamman a siyasar jihar Kano, wadda ake yi wa kirari da “Iya mata sai ɗan Kano.”
Sau biyu Ganduje na yi wa Kwankwaso mataimakin Gwamnan, sannan ko lokacin da Kwankwaso ya rabu da mulki a zangonsa na farko ya ja Ganduje a jiki, wajen yin aiki tare da shi a damarmakin da ya samu.
Sai dai dangantaka tsakanin ‘yan siyasar biyu ta yi tsami a lokacin da Ganduje ya zama gwamnan jihar Kano, inda a ka rika samun takun saka a tsakaninsu.
Wannan rashin fahimtar juna ta yi kamarin da ta tilasta wa Kwankwaso ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano, inda ya koma PDP mai adawa, ya kuma yaƙi Ganduje a zaben gwamnan jihar na shekarar 2019.
A hirar tasa da BBC Hausa, tsohon gwamnan na Kano Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna takaicinsa kan yadda rikicin shugabancin ke kara kamari a jam’iyyarsu ta PDP, wadda ke da burin karbar mulki a hannun APC a kakar zaben 2013.
A cewar Kwankwaso, duk rashin gogewa ne da rashin iyawa ya haifar da wannan rikici, shu shugaban nan Secondus saura wata daya ko daya da wani abu ya sauka, kamar yadda tsarin mulki ya tanada, yawanci rashin hakuri ne ke kawota.
“A yanzu masu karfi a jam’iyya wannan ya ja nan wannan ya ja nan, karshenta abun da zai faru shine sai a yaga ta gaba daya, kaga sakamakon ba zai taimaka mana ba tunda bamu da shugaban kasa, ba mu muke da yawancin gwamnoni ba,” in ji Kwankwaso.
A cewar Kwankwaso shi ba abin da ya shafe shi da rikicin jam’iyyar, domin ya yi imanin cewa babu bukatar a yi shi, rashin fahimar lamura ne kawai irin na wasu.