World Youths Day : Masana a Najeriya na ganin halin da matasan ƙasar ke ciki abin a tausaya ne.

Yau ce ranar matasa ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta keɓe domin tunawa da muhimmancin da miliyoyin matasan a faɗin duniya ke da shi, da kuma irin rawar da za su iya takawa a cikin al’umma matsawar aka ba su dama. 

Taken wannan rana a bana shi ne ‘Rawar da matasa za su iya takawa wajen samar da abinci da kuma kyautata muhalli’.

To amma yayin da ake buƙatar matasan su taka rawa don ci gaban ƙasashensu, masana a Najeriya na ganin halin da matasan ƙasar ke ciki abin a tausaya ne.

Kuma kafin ma su iya ba da gudummawarsu akwai buƙatar a fara ba su gudunmawa.

Wane irin taimako matasa a Najeriya ke buƙata?

Abu ne a zahiri rashin aikin yi ya yi katutu a Najeriya a dalilin matsin tattalin arziki da ƙasar ta samu kanta.

A cewar Dr. Hussaini Abdu na ƙungiyar jin ƙai ta Care International, matasa a Najeriya su ne suka fi jin jiki a harkokin rayuwa na yau da kullum saboda rashin aikin yi.

”Yanzu idan ka duba a Najeriya ƙididdiga na nuna cewa rashin aikin yi ya kusa kai wa kashi 40 cikin 100.

”Kuma rawar da matasa ke takawa a harkokin siyasa ko shugabanci a Najeriya ba wata babba ba ce.”

”Idan ka duba misali tun daga ministoci da kwamishinoni har ma da ƴan majalisar tarayya da na jihohi za ka ga ba kasafai ake samun matasa a ciki ba,” in ji masanin.

Ina mafita?

Sai dai Dr Abdu ya jinjinawa gwamnatin tarayya a ƙoƙarinta na fito da shirye-shiryen tallafawa matasan don su dogara da kansu.

Amma kuma a cewarsa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka, don kuwa akwai buƙatar sauran masu ruwa da tsaki su riƙawa gwamnatin domin kuwa yaƙin ya fi ƙarfinta ita kaɗai.

Masanin ya kuma nuna damuwa kan yadda gwamnatocin jihohi da yan kasuwa da bankuna ba sa tausaya wa matasan, kuma ba sa riƙawa gwamnatin tarayya wurin agazawa matasa su sami abin yi.

A cewarsa ya kamata suma su fito da shirye-shirye da za su taimakawa matasa a matakin jihohi don ragewa gwamnatin tarayya aiki.

Ya kuma yi kira ga matasan da su rungumi noma da sauran sana’o’i a maimakon jiran aikin ofis.