Wata ɗalibar Chibok ta miƙa wuya ga sojoji tare da gogarman Boko Haram ɗin da ya aure ta auren-dole
Tsohuwar ɗaliban Chibok da ke cikin ɗalibai sama da 200 ɗin da Boko Haram su ka sace a cikin 2014, ta miƙa wuya ga sojoji tare da ɗan Boko Haram ɗin da aka yi mata auren-,dole da shi a sansanin su.
Rahotanni sun tabbatar da cewa miji da matar sun yi saranda ga sojojin da ke ɗaya daga cikin sansanonin da ke yankin Tafkin Chadi.
An dai sace ɗaliban sama da 200 a cikin 2014, amma a karɓo wasu. Sai dai kuma an haƙƙaƙe cewa akwai akwai kamar guda 100 da har yanzu su na a hannun ‘yan ta’addar.
Majiya ta ce da dama daga cikin ‘yan Boko Haram da ‘yan ta’addar ISWAP na ta miƙa tayin yin saranda ga sojojin Najeriya tare da ajiye makaman su.
“Yan ta’addar sun yanke shawarar yin tururuwar miƙa wuya ne musamman ganin yadda sojoji ke yi masu ruwan wuta ta sama da ta ƙasa da kuma ɓarkewar cuta mai kisa a cikin su. Sai kuma matsanancin ƙarancin abinci da su ke fama da shi.
“Akwai masu ƙoƙarin yin saranda sosai, amma dai bisa dukkan alamu sojojin Najeriya na ci gaba da matsa masu ƙaimi har sai-baba-ta-gani, saboda dalilai na tsaro.” Inji wani jami’in.
Ba a samu jin ta bakin Kakakin Sojoji Onyeama Ugochukwu ba, ballantana a ji daga gare shi takamaiman labarin sarandar da aka yi ɗin.
Boko Haram da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun hana ƙasar nan zaman lafiya shekaru masu yawa.