Wata Kungiyar Fafutuka Na Shirin Gudanar Da Gangami a Jamhuriyar Nijar

Wata kungiyar fafutuka ta TLP ta kudiri aniyar gudanar da taron gangami a ranar Juma’a a birnin Yamai da nufin ta da mahukunta daga barci akan matsalolin tsaro da wasu batutuwa. 

Kungiyar ta dauki niyyar kalubalantar hukumomi ne akan matsalolin dake da nasaba da lalacewar al’amuran tsaro amma wasu kungiyoyin na daban na cewa tara dimbin mutane a wuri guda a yanayin da ake ciki a Nijar na iya zama barazana.

Gangamin wanda kungiyar Tournons La Page ta Shirya gudanarwa daga karfe uku na ranar Juma’a 11 ga watan Fabrairu a dandalin Place de la Conceration dake gab da majalisar dokokin kasar a Yamai wata dama ce da shugabanin kungiyar ke son amfani da ita domin bayyana wa hukumomin Nijar damuwarsu a game da tarin matsalolin da suka ce suna addabar jama’ar kasar a cewar shugabansu Maikol Zody.

Sai dai a wani abinda ke fayyace rarrabuwar kawunan dake tsakanin jami’an farar hula wasu kungiyoyi na daban mambobin gamayyar Convernace Democratique a wata sanarwar da suka fitar sun gargadi mahukunta su hana gudanar da wannan taro saboda a tasu fahimta ba za a rasa wata manufar boye ba. 

A karshen watan Janairu da ya gabata hukumomin birnin Yamai sun soke wata zanga zangar da kungiyar Tournons La Page ta tsara a nan Yamai da zummar kalobalantar gwamnatin Nijar da suke zargi da gazawa a fannoni da dama ciki har da sha’anin tsaro da yaki da cin hanci. 

Mahakamancin wannan mataki ya shafi jam’iyar PNDS mai mulki wacce ita ma magajin garin Yamai ya hana magoya bayanta gunadar da bikin cika shekaru 31 da kafuwar jam’iyar saboda dalilan tsaro da na barazanar yaduwar anobar coronavirus mako guda kenan bayan da shugaban kasa Mohamed Bazoum ya yiwa wasu kungiyoyi alkawarin bai wa kowane dan kasa ‘yancin gudanar da zanga zanga muddin aka shirya abin ta hanyar doka.