Wannan kisa ba za mu bari ba kuma ba za mu yi shiru ba : Bala Lau

Ƙungiyar Izala a Najeriya ta yi kira ga hukumomin ƙasar su gaggauta gudanar da binciken ƙeƙe-da-ƙeƙe tare da tabbatar da ganin sun hukunta duk masu hannu a kisan gillar da aka yi wa fitaccen malamin nan na Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.

An kashe malamin ne a ranar Jumma’a, inda rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta tabbatar da cewa wasu sojoji biyu ake zargi da kisansa.

Shugaban ƙungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya shaida wa Jaridar BBC cewa kisan da aka yi wa malamin ta’addanci ne babba a kan al’ummar musulmi baki daya.

Ya ce “A duk lokacin da aka rasa wani malami jigo, to an yi babbar asara ce ga al’umma baki daya.”

Sheikh Bala Lau ya ce abin takaicin shi ne hanyar da aka bi wajen kisan malamin, domin hanya ce da kowanne musulmi zai nuna bakin cikinsa da alhininsa kan abin da aka aikata don kisan gilla ne.

Ya ce “Mu a matsayinmu na wannan kungiya, to muna kira ga gwamnatin tarayya a kan ta dauki mataki wurin gano da kuma daukar mataki kan wadanda suka aikata wannan ta’addanci kuma menene manufarsu? Kuma me ake so a jefa wa alumma?”.

Sheikh Bala Lau ya ce “Wannan kisa ba za mu bari ba kuma ba za mu yi shiru ba za mu ci gaba da neman hakkin wannan malami.”

Shugaban kungiyar Izalar ya ce suna so a dauki matakin da ya dace bisa la’akari da dokokin kasa da kasa.

Haka Al’ummar Muslim da Dama suna ta Nuna Takaicinsu kan abinda yake faruwa a kasar wajen nuna bambanci Idan anyi wa ‘yan Arewa ta’addanci Makamancin wannan, sun ce ba kasafe Gwamnati take Daukar Hukunci ba sabanin idan abokan zaman su na Kudu aka taba

Wani malamin Addini a sokoto wato Sheikh Murtala Bello ya Bayyana cewa Anmayar da rayukan Jama’ar Arewa ba abakin kowa ba muamman yadda aka yi Afuwa ga Danta’adda Bello Turji, sannan ya nuna takaicinsa ga manyar Arewa wajen ko-inkula da abinda ya shafi jama’arsu, ya ce sun fi mayar da hankali wajen Siyasarsu da neman abin duniya.