Wani magidanci ya roki kotu ta tilasta wa matarsa ta biya shi kudin rabuwar aure naira 200,000

A ranar Laraba ne wani magidanci mai suna Abdullahi Mustafa ya umarci matarsa Asma’u Muhammad ta biya shi Naira 200,000 kafin idan tana so ya sake ta.

Mustafa ya fadi haka ne a zaman sauraren karar neman a rabu da Asma’u ta shigar a kotun Magajin gari dake Kaduna.

Asma’u da Mustafa sun yi zaman aure na tsawon shekaru 10, amma kuma gaba ɗaya sai ta ji kaunarsa ya fice daga zuciyarta, ta ga abinda ya fi dacewa su yi shine kowa ya kama gabansa kawai.

Sai dai kuma Asma’u ta ce a shirye take ta maida wa Mustafa kudin sadakinsa Naira 20,000.

“Bana son in jefa kaina cikin fushin Allah, in rika samun tsinuwar mala’iku saboda na yi wa mijina rashin biyyaya”.

Shi kuwa Mustafa ya ce ba zai karbi Naira 20,000 ba saboda ba za su Isa ya auri wata matar ba.

“Darajar kudi a da ba daya yake da darajar su a yanzu ba. Saboda haka don na biya naira 20,000 yanzu darajar ta a lokacin ya kai naira 200,000.

“Zan saki Asma’u idan ta amince ta biya ni Naira 200,000 ba 20,000 ba.

Alkalin kotun Murtala Nasir ya dage shari’ar zuwa 9 ga Agusta.

Bayan haka, Kotun Majistare na magajin Gari a Kaduna, ta yanke wani hukunci mai kama da irin wannan, sai da wannan karon Bilkisu da Bello sun nemi su hakura da juna ne saboda Kaunar da ke tsakanin su ya rikide ya zama gaba.

Alkalin kotun Nuhu Falalu ya yanke hukuncin cewa Bilkisu za ta mayar wa Musa kudin sadakin sa naira 20,000.

Lauyan dake kare Bilkisu M.B. Alhassan ya ce Bilkisu tana nemi kotu ta raba auren ta da Musa ne saboda bata kaunar sa a matsayin miji kuma.

Musa wanda matarsa ta tabbatar cewa bai taba cin mutuncin ta ba ya amince kotu ta raba auren.