Wani Ma’aikaci Ya na Neman Saki Akan Zargi
Wani ma’aikacin gwamnati, Mista Nnadi Onu, a ranar Laraba, ya roki wata kotun al’ada da ke Jikwoyi, Abuja, da ta ba shi damar saki a bisa dalilin cewa matarsa,…

Wani ma’aikacin gwamnati, Mista Nnadi Onu, a ranar Laraba, ya roki wata kotun al’ada da ke Jikwoyi, Abuja, da ta amince masa da damar yin saki bisa zargin da matarsa ke yi, Ogechukwu ta zarge shi da neman yin amfani da ita wajen ibada.
Onu ya shaida wa kotun cewa, “Ban san dalilin da ya sa take zargina da irin wannan abu ba. Wannan ya nuna babu sauran amana a tsakaninmu.”
Ya kuma shaida wa kotun cewa, jim kadan bayan zargin na yi rashin lafiya kuma aka gano cewa na dauke da gubar abinci.
Ya kara da cewa, “Ita ma bata da mutunci. Yan uwana sun daina ziyarta na, don haka na ƙaura. A kan wannan ne nake neman a raba auren nan.”
Sai dai Ogechukwu ya musanta zargin.
Alkalin kotun, Labaran Gusau, ya dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Nuwamba (NAN)