Wani jirgin fasinja ya tarwatse a Turkiyya
Wani jirgin sama ya jirkice a wata tashar jiragen sama da ke Turkiyya inda ya tarwatse tare da raunata mutum 21, a cewar jami’ai.
Jirgin a cewar rahotanni yana dauke da fasinjoji 171 da ma’aikatan jirgin shida lokacin da ya fado a filin jirgin saman Sabiha Gokcen a Santanbul.
Ministan sufuri Mehmet Cahit Turhan ya ce ba a samu asarar rai ba.
Gwamnan Santanbul Ali Yerlikaya ya ce an garzaya da mutum 21 asibiti sannan ana ci gaba da kwashe mutanen da abin ya rutsa da su.
Jirgin na Pegasus Airlines ya sauka ne cikin mamakon ruwan sama bayan ya tashi daga lardin Izmir kamar yadda kafafen yada labaran Turkiyya suka rawaito.
Jami’ai kuma na ci gaba da kokarin zakulo wadanda suka makale cikin jirgin.
Hoton bidiyo da ke watsuwa a shafukan sada zumunta ya nuna wuta ta tashi a jirgin saman sai dai daga bisani masu kashe gobara sun kashe wutar.