Uganda ta killace mutum 100 saboda coronavirus
Ma’aikatar lafiya ta kasar Uganda ta ce an killace sama da mutum 100 da suka isa kasar daga China domin hana bazuwar cutar coronavirus.
Ministar lafiya Dr Jane Aceng ta fada wa manema labarai a Kampala, babban birnin kasar, cewa 44 daga cikin mutanen da aka killace ‘yan China ne.
Ta kuma ce ma’aikatar ba ta da masaniyar wani dan kasarta da ake zargin ya kamu da cutar.
Kasar ta kuma tsananta matakan tantance mutanen da suke shiga kasar sannan ta bukaci matafiyan da suka fito daga China su gabatar da bayanansu domin jami’an lafiya su duba su.
Gwamnatin ta ce akwai daruruwan daliban Uganda a China amma ta ce babu wani shirin kwashe su daga kasar.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta nemi tallafin dala miliyan $675, kwatankwacin kusan naira biliyan 245, domin yaki da cutar coronavirus ta hanyar zuba hannun jari a kasashen da suke cikin hadarin kamuwa da cutar.
Shugaban WHO Tedros Ahanom Ghebreyesus ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na duniya da aka gudanar a Geneva babban birnin kasar Switzerland.
Ya ce milyan $60 na kudin zai zama na amfanin WHO, yayin da ragowar kudaden kuma za a taimaka wa kasashe don kare su daga coronavirus.
A cewarsa, WHO za ta aike takunkumin kariya 500,000 da abin shakar iska 40,000 zuwa ga kasashe 24.
Tedros ya kuma yaba da tallafin miliyan $100 daga gidauniyar Bill and Melinda Gates domin yin gwajin cutar da kula da masu ita da kuma bincike kan maganinta.