Kasar Uganda ta kaddamar da hare-hare ta sama, da kuma na makaman atilari kan kungiyar ‘yan tawayen ‘Allied Democratic Forces’ (ADF) da ke gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
Cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter ministan sadarwar gwamnatin Congo Patrick Muyaya, ya ce Uganda ta kaddamar da farmakin a yau Talata ne bayan cimma yarjejeniyar da bangarorin biyu suka yi.
Harin dai ya zo ne kwanaki biyu bayan da wata majiya mai tushe a kasar ta Congo ta bayar da rahoton cewa, shugaban Felix Tshisekedi ya bai wa Uganda izinin afkawa kungiyar ADF da ke da sansani a kasar tasa, wadda aka zarga da kai hare-haren kunar bakin wake a birnin Kampala.
Kungiyar ADF da Amurka ke dangantawa da kungiyar IS, ta kafu ne cikin shekarar 1995 a gabashin Jamhuriyar Congo, a karkashin wata hadakar ‘yan tawayen Uganda da ta kunshi Musulmi masu adawa da shugaba Yoweri Museveni.
Sannu a hankali ne dai kungiyar ‘yan tawayen ta ADF ta zama mafi tsananin barazana a yankin Kivu da ke gabashin Jamhuriyar Congo da ya dade ya na fama da rikici, inda mayakanta suka kashe dubban fararen hula musamman a yankin Beni.
Tun daga watan Afrilun shekarar 2019, kungiyar IS ta dauki alhakin wasu hare-hare da ADF ta kai, tare da bayyana ta a matsayin reshenta na lardin tsakiyar Afirka.