Tsugune ba ta ƙare ba bayan rushe SARS
Duk da sanarwar da Sufeto Janar na ƴan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya bayar ta rushe rundunar SARS mai yaƙi da ‘yan fashi, har yanzu daina zanga-zangar nuna ɓacin rai ba ta dakata ba sakamakon sababbin buƙatun da ‘yan Najeriya suka miƙa wa gwamnati.

Shahararren mawaƙi ɗan Najeriya da aka fi sani da Davido ya ce zai yi wata ganawa ta musamman da Sufeto Mohammed Adamu a safiyar Litinin tare da kira ga abokansa da su yi wa Abuja tsinke domin halartar ganawar.
Daga cikin sharuɗɗan da yake nema daga gwamnati, Davido na son gwamnati ta yi dokar da za ta hukunta ‘yan sandan da suka ci zarafin ‘yan Najeriya.

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1
Zanga-zangar ta fi ƙarfi a Abuja, babban birnin ƙasar da kuma Legas. Wani matashi ya rasa ransa a wurin zanga-zangar ta ranar Asabar Jihar Oyo.

Tuni ƙungiyar da ke sa ido kan ayyukan gwamnati da yaƙi da laifukan rashawa ta SERAP ta yi kira ga ƙungiyar Commonwealth ta ƙasashe rainon Ingila da ta hukunta Najeriya kan cin zarafin da ‘yan sanda suka yi wa masu zanga-zangar.
Idan ba a manta ba, ranar Lahadi ne gwamnatin Najeriya ta miƙa wuya ga buƙatar ƙasar, inda Mohammed Adamu ya ce an rusa ayyukan rundunar SARS a faɗin ƙasar sannan kuma za a haɗe su da sauran ‘yan sanda.
Hakan ya biyo bayan kusan mako biyu da aka shafe ana zanga-zanga a fili da kuma shafukan zumunta, suna zargin rundunar da cin zarafi da cin hanci da azabtar da mutane, ta hanyar amfani da maudu’ai daban-daban irinsu #EndSars.
Daga cikin masu zanga-zangar a shafukan zumunta har da Zahra Buhari, ‘ya ga Shugaba Buhari, da ‘yar mataimakinsa Kiki Osinbajo, da sauran taurarin fina-finai da ‘yan ƙwallon ƙafa da mawaƙa a faɗin duniya.
Sabbin buƙatu biyar na masu zanga-zanga

Buƙatun na ƙunshe ne cikin wani hoto da ya karaɗe shafukan zumunta ranar Lahadi jim kaɗan bayan rushe rundunar.
- A saki dukkanin masu zanga-zangar da aka kama
- A gurfanar da dukkanin ‘yan sandan da suka ci zalin ‘yan Najeriya sannan a biya iyalansu diyya
- A kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai sa ido kan binciken cin zarafi da ‘yan sanda suka aikata da kuma hukunta su cikin kwana 10
- A yi wa dukkanin dakarun rundunar SARS gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa kafin sauya musu wurin aiki
- A ƙara wa ‘yan sanda albashi.