Tinubu Yayi Sabbin Nade-nade a ofishin mataimakin Shugaban kasa

Shugaban kasar Nigeria Bola Tinubu ya nada Kingsley Stanley Nkwocha, tsohon Manaja kuma Editan Jaridar Leadership, a matsayin Babban Mataimaki na Musamman (SSA) kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa a Fadar Shugaban Kasa.

An nada Nkwocha ne tare da wasu da dama da za su yi aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa.

Tinubu ya kuma nada Tope Fasua, babban jami’in gudanarwa na Global Analytics Consulting, a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki a ofishin mataimakin Shugaban kasa .

A cikin jerin sunayen, wasu da aka nada a ofishin mataimakin shugaban kasar sun hada da Sadiq S Jambo a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, Dr. Muhammad Bulama, a matsayin babban mataimaki na musamman kan aiyuka na musamman, Mahmud Muhammad a matsayin mataimaki na musamman na cikin gida, da Ahmed Ningi a matsayin babban mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai na zamani da bada agajin gaggawa.

Sauran su ne Stanley Nkwocha mataimakin na musamman kan harkokin yada labarai a ofishin mataimakin Shugaban kasa, sai Tope Kolade Fasua, Mashawarci na Musamman Tattalin Arziki da Sadiq S Jambo Mai baiwa mataimakin Shugaban kasa Shawara kan harkokin tattalin arziki.

Gimba Kakanda, marubuci kuma manazarci kan harkokin jama’a, Tinubu ya nada shi a matsayin Babban Mataimaki na Musamman, kan harkokin Bincike da fashin baki a ofishin mataimakin Shugaban kasa.

Sai Dr. Hakeem Baba Ahmad a matsayin Mai baiwa mataimakin Shugaban kasa Shawara kan harkokin siyasa da Kuma Dr. Aliyu Moddibo mai baiwa mataimakin Shugaban kasa Shawara kan dukkanin al’amura.