Tinubu Yayi Aikin Umarah A Makkah

Tinubu Yayi Aikin Umarah A Makkah

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Lahadin da ta gabata, lolacin da yake yin karamar Hajji (Umrah) a Makkah, ya yi addu’ar Allah ya shiryar da Nijeriya.

Shugaban ya fara gudanar da ibadar addinin muslunci ne bayan kammala aikinsa a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya inda ya halarci taron Saudiyya da Afirka.

Babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Abdulaziz Abdulaziz ne ya bayyana manufar shugaba Tinubu zuwa kasa mai tsarki domin aikin Umrah a yammacin Lahadin da ta gabata.

A cewarsa, a wannan tafiya ta ruhaniya, shugaban ya yi addu’o’in samun ci gaba a Najeriya tare da neman tsarin Allah domin ya jagoranci kasar.

Mai Girma Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya dauki hutu ne a karshen aikinsa a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, domin sauke farali na aikin Hajji (Umrah) da safiyar yau a birnin Makkah. Ya yi amfani da wannan damar wajen yi masa addu’a ga daukakar Najeriya da kuma shiriyar Ubangiji,” in ji Abdulaziz.