Takaitattun Labaran Yammacin Talata

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta fara raba Katin Zaɓe na Dindindin (PVC) a cikin Oktoba da kuma Nuwamba, tare da kakkaɓe sunayen duk waɗanda suka yi rajista sau biyu ko fiye da haka.

Akalla mutum hudu aka kashe aka yi garkuwa da wasu shida, a lokacin da yan bindiga suka kai hari a kasuwar Jauro Manu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.

Wata Babbar Kotun Shari’a da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, ta raba auren wani mutum mai suna Alhaji Musa Tsafe wanda ya auri jikarsa shekaru 23 da suka gabata.

Bayan shafe shekaru yana adawa da Buhari, Orubebe ya Koma APC.

Shugaban Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) Farfesa Mansur Bako Matazu, ya gargadi ’yan Najeriya da su shirya fuskantar karin ambaliyar ruwa a watanni biyu masu zuwa.

Mutane 16 Sun Mutu, 5 Sun jikkata a Hatsarin Mota A Legas.

Sanatan APC mai wakiltar Bauchi ta Arewa a Majalisar Dattawa, Adamu Bulkachuwa, ya ce akwai takwarorinsa da dama da ke goyon bayan yunkurin tsige Muhammadu Buhari daga shugabancin Najeriya.

An kama wasu mutum biyu da suka yi amfani da wata budurwa mai suna Beatrice Adah mai shekara 23 da ke fama da cutar kansa har suka tara kudin da suka gina gida a Abuja.

2023: Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya gana da gwamnonin APC a gidansa da ke Jihar Legas, gabanin fara shirye-shiryen shiga yakin neman zabensa.

Gwamnatin Edo ta rushe masallaci da kasuwar ‘yan Arewa.

An gurfanar da mutum 84 da aka kama bisa zargin yi wa wasu mata su takwas fyade lokaci daya a wani wajen daukar bidiyon raye-raye a Afrika ta Kudu.

Tsohon dan wasan gaban Afrika ta Kudu Benni MacCarthy ya samu shiga tawagar masu horar da Manchester United.

Dan kwallon Liverpool, Diogo Jota ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa karshen kakar 2027.