Takaitattun Labaran Yammacin Laraba
Shugaban sajojin sama na Najeriya (NAF) ya umarci Sojoji su Ragargaji ‘Yan Ta’adda, Ba Sani Ba Sabo”.
Hukumar da ke Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC) ta sanya wa gidan talabijin na Trust TV tarar Naira miliyan biyar saboda yin rahoton binciken kwakwaf kan ayyukan ’yan bindiga.
Domin sake salo wajen ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda a sassan Najeriya, Rundunar Sojojin Sama ta kaddamar da wata sabuwar runduna.
Jami’an Hukumar Kwastam sun cafke wasu kayayyakin da aka yi fasa-kwauri da kudinsu ya kai Naira miliyan 232 a jihohin Adamawa da Taraba.
’Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin awon gaba da shugaban Makarantar Kididdiga ta Gwamnatin Tarayya da ke Manchok, hedkwatar karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.
’Yan kabilar Kwayam da ke Gabashin jihar Borno sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram su tara ta hanyar harbi da kibiya a wata arangama a ranar Laraba.
Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda (AIG) mai kula da shiyya ta 12 mai hedikwata a Bauchi, Audu Adamu Madaki, ya ji rauni Bayan tsallake rijiya da baya Inda wasu ‘yan bindiga suka kai wa tawagarsa hari a jihar Kaduna, inda rahotanni suka tabbatar da kashe dogarinsa.
Alkalin alkalan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Mai Shari’a Kashim Zannah, ya rantsar da alkalan Shari’ar Musulunci 21 a jihar.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta tabbatar da kisan wasu mutum bakwai da ake zargin ’yan ta’addan IPOB da aikatawa.
Shugaban Buhari ya ranstar da sabbin manyan sakatarori na wasu ma’aikatu a Najeriya a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba.
Fasinjan jirgin kasan da ’yan bindiga suka sako ya ce har yanzu ba a cire harsashin da suka harbe shi daga cikinsa ba.
Jamhuriyar Nijar ta cika shekara 62 da samun ‘yancin kai daga Turawan Faransa a yau Talata.
Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce ”ba zai amince” da dabi’ar wasu ‘yan wasa har da Cristiano Ronaldo da suka bar Old Trafford tun kan tashi daga wasan sada zumunta ranar Lahadi.