Labaran Najeriya Na Yau – 5 Ga Junairu, 2026
1. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa mutane 25 sun mutu, yayin da 14 suka ɓacesakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a ƙaramar hukumar Nguru ta Jihar Yobe. NEMA ta ce an ceto mutane 13 bayan hatsarin da ya faru da misalin ƙarfe 7:48 na yammacin Asabar.
2. Masu garkuwa da mutane da suka sace ‘yan’uwa biyu, Ibrahim da Tahir Abu, a Auchi da ke ƙaramar hukumar Etsako West, sun nemi kuɗin fansa har Naira miliyan 200. Mahaifinsu, Momoh Tahir, ya ce masu garkuwar sun tuntubi iyali da safiyar Lahadi domin neman kuɗin.
3. An yi taron jana’iza mai cike da alhini a London a ranar Lahadi, 4 ga Janairu, 2026, yayin da iyalai da abokai suka taru domin sallar jana’izar Sina Ghami da Abdul Latif Kevin Ayodele, abokan kusa na fitaccen ɗan damben boksin duniya, Anthony Joshua. An kuma gudanar da taron wake a Cavendish Banqueting Hall, sannan aka yi jana’izar Ghami a Hendon Cemetery da Crematorium.
4. Akalla mutane 60 sun mutu a wani mummunan hari da aka kai Kasuwan Daji da ke ƙaramar hukumar Borgu ta Jihar Neja. Rahotanni sun ce ‘yan ta’adda daga Gandun Dajin Kainji sun kai harin da misalin ƙarfe 4 na yamma, inda suka kewaye kasuwar, suka kashe ‘yan kasuwa da masu sayayya tare da sace wasu da dama, musamman mata da yara.
5. Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na Rwanda, Shugaba Paul Kagame, sun yi wata ganawa ta sirri a Paris, Faransa, a ranar Lahadi. Rahotanni sun ce sun tattauna batutuwan duniya da dabarun ci gaban muradun Afirka.
6. Bayan kama kilo 31.5 na hodar iblis (cocaine) a cikin jirgin ruwa MV Aruna Hulya a tashar GDNL, Apapa, Lagos, a ranar Juma’a 2 ga Janairu, 2026, Hukumar NDLEA ta tsare ma’aikatan jirgin ‘yan Indiya 22. Daraktan yada labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ne ya tabbatar da hakan.
7. Wani hatsarin mota a ƙaramar hukumar Langtang North ta Jihar Plateau ya yi sanadin mutuwar mutane biyar, yayin da 13 suka jikkata. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wani mummunan hatsari a Jos da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu.
8. Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi, SAN, ya dakatar da tuhumar ɓata suna da aka shigar wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. An shigar da sanarwar dakatar da shari’ar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
9. Shugabannin jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Ahoada West ta Jihar Rivers sun ce za su bi duk umarnin da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayar gabanin zaɓen 2027. Shugaban jam’iyyar na yankin, Rejoice Otobo, ya bayyana hakan yayin ziyarar godiya da Wike ya kai yankin.
10. Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP sun shimfiɗa sharudda masu zurfi domin sulhu yayin da ake ƙara tattaunawa don warware rikicin cikin gida na jam’iyyar. Batutuwan tsarin jam’iyya, yiwuwar sake taron ƙasa, neman afuwa a bainar jama’a, da sauye-sauye masu muhimmanci suna cikin muhimman abubuwan da ake tattaunawa.
