1. Jami’an hukumar EFCC sun kai samame a ɗakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library, Abeokuta, Jihar Ogun, inda suka cafke wasu matasa da ake zargi da damfarar yanar gizo. An ce EFCC ta gudanar da wannan samame ne da safiyar Lahadi.
2. Fadar shugaban ƙasa ta karyata jita-jitar cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana da rashin lafiya. Wannan martani ya biyo bayan wani rahoto daga ICIR da ya ce tawagar likitocin shugaban na shirin kai shi ƙasashen waje domin gaggawar jinya.
3. Wata yar aikin NYSC mai suna Rita Uguamaye ta haifar da sabon ce-ce-ku-ce bayan ta zargi hukumar da hana ta takardar kammala hidima duk da cewa ta kammala shekarar hidimarta. Uguamaye, wacce aka fi sani da “Raye”, ta yi hidima a Jihar Legas, kuma ta yi fice bayan wani bidiyo da ta wallafa a TikTok tana sukar gwamnatin Tinubu ya bazu.
4. Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya sallami wasu kwamishinoni da mataimakan musamman daga majalisar zartarwar jihar. Sakatariyar gwamnati, Farfesa Habibat Adubiaro, ta ce sallamar ta fara aiki nan take. An umarci wadanda abin ya shafa da su mika ofis ga babban sakatare ko babban jami’in ma’aikatarsu.
5. Kungiyar Middle Belt Forum (MBF) ta bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Mista Peter Obi, mutum ne mai gaskiya wanda za a iya amincewa da shi wajen cika alkawarin yin wa’adin shekara hudu kacal idan aka zabe shi a 2027.
6. Wasu ‘yan daba dauke da adda sun kai wa direban mota mai suna Dallami Yunusa hari a Ogi Junction, Okigwe, Jihar Imo, inda suka jikkata shi sannan suka ƙona motarsa. Shugaban NURTW reshen manyan motoci a Okigwe, Dahiru Musa Raza, ya tabbatar da lamarin.
7. Rundunar sojojin Najeriya ta kashe ‘yan ta’adda guda biyar ciki har da wani kwamanda da ake nema ruwa a jallo, tare da ceto wadanda aka yi garkuwa da su a hare-haren yaki da ta’addanci a sassan ƙasar. Kakakin rundunar, Laftanar Kanal Apollonia Anele, ya ce an kuma samu makamai da harsasai daban-daban.
8. Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Rivers na kara samun karbuwa, inda yanzu tana da mambobi sama da 800,000. Mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Luckyman Egila, ya bayyana haka a taron manema labarai a Fatakwal.
9. Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Delta ta kama wani da ake zargi da fashi da makami mai suna Chinedu Eze, tare da kwato wata motar Mercedes-Benz GLK da aka sace a Asaba. Kakakin rundunar, SP Bright Edafe, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.
10. Ministan Sufurin Jiragen Sama da Cigaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya sanar da dakatar da yajin aikin da ƙungiyoyin ma’aikatan jiragen sama suka shirya fara ranar Litinin. Ya bayyana a shafinsa na X cewa hakan ya biyo bayan shiga tsakani da ya yi.