Site icon TWINS EMPIRE

Takaitattun Labaran Safiyar Yau Alhamis 14, Aug. 2025

Labaran Najeriya Na Yau – 14 ga Agusta, 2025

Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta sanya takunkumin shekaru bakwai kafin a ƙirƙiri sababbin makarantun gaba da sakandire na tarayya. Wannan ya haɗa da jami’o’i, kwalejojin fasaha (polytechnic) da kwalejojin ilimi.

2. Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja ranar Alhamis zuwa kasashen Japan da Brazil. Kakakin shugaban ƙasa kan harkokin bayani, Bayo Onanuga, ya ce shugaban zai tsaya a Dubai, UAE, kafin ya wuce Japan.

3. Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau, na tsawon watanni uku domin gudanar da bincike kan zarge-zargen rashin da’a, cin zarafi da karkatar da kuɗaɗe da kansilolinsa suka yi masa.

4. Gidan karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library a Abeokuta, Jihar Ogun, ya nemi diyya ta Naira biliyan 2.5 daga hukumar EFCC kan samamen da ta kai ranar 10 ga watan Agusta. Sun ce hakan ya lalata musu suna, kasuwanci, da matsayin kuɗi na tsohon shugaban ƙasa Obasanjo.

5. Gwamnatin Tarayya ta rage takunkumin hana jirgin sama kan mawakin Fuji, Wasiu Ayinde (KWAM 1), zuwa wata guda. Da farko an hanashi zirga-zirgar jirgin sama na cikin ƙasa har na tsawon watanni shida saboda zargin rashin da’a a filin jirgin sama na Abuja.

6. Hukumar DSS ta kama wani shugaban ‘yan ta’adda, Abubakar Abba, wanda ake zargin jagoran kungiyar ta’addanci ta Mahmuda. Kungiyar ta dade tana addabar yankin Borgu a Jihar Neja da kewaye, da kuma wasu sassan Jihar Kwara.

7. Rundunar ‘yan sanda a Jihar Imo ta kama wani fasto mai suna Ikenna Emmanuel kan zargin yi wa wata budurwa ‘yar shekara 20 fyade a yankin Orlu. An kuma kama wani mutum mai suna Franklin Chizoba da ake zargin ya taimaka masa wajen aikata laifin.

8. Shugaba Bola Tinubu a ranar Laraba ya umarci a sake nazarin tsarin cire kuɗi da riƙe kuɗaɗen shiga na manyan hukumomin tara kuɗin shiga na ƙasa, domin ƙara adana kuɗaɗe, inganta kashe kuɗi, da samun kuɗaɗe don ci gaban ƙasa. Hukumomin sun haɗa da FIRS, Hukumar Kwastam, NIMASA, da NNPC Limited.

9. Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Imo ta kama wani mutum mai shekara 39, Ifeanyi Odinka, bisa zargin kashe mahaifinsa, Dennis Odinka, bayan sun yi saɓani kan kudin siyar da fili a Orlu. An ce ya yi masa yanka har lahira bayan faɗa kan kudin filin.

10. Hukumar JAMB ta sanar da shirin tantance sama da ɗalibai 500 masu hazaka ƙasa da shekaru 16 da ke neman shiga jami’a a shekarar karatun 2025/2026. Za a gudanar da tantancewar daga 22 zuwa 26 ga watan Satumba ta hannun wani kwamitin musamman na fasaha.

Exit mobile version