Labaran Najeriya Na Yau – 29 Ga Agusta, 2025
1. DSS ta gurfanar da mutum 9 a kotu kan kisan gilla a Benue da Plateau
Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da mutane tara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin hannu a kashe-kashe a Yelwata, Guma LGA ta Jihar Benue, da kuma wasu sassa na Jihar Plateau. Rahotanni sun ce hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.
2. Shugaban NNPC ya ce ana kai wa kamfanin hari
Shugaban rikon amana na kamfanin NNPC Ltd., Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya ce akwai wasu da ke adawa da sauye-sauyen da ake gudanarwa a kamfanin. Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi tawagar ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (PENGASSAN) a NNPC Towers Abuja.
3. Amaechi ya ayyana cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027
Tsohon Ministan Sufuri kuma jigo a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027. Ya yi wannan furuci ne a Kano bayan ganawa da wata ƙungiyar ’yan kasuwa.
4. Sojoji da DSS sun kashe ’yan bindiga 50 a Jihar Neja
Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an tsaro sun hallaka aƙalla ’yan bindiga 50 a Kumbashi, karamar hukumar Mariga, Jihar Neja.
5. Kwankwaso ya ce ba zai bar NNPP ba
Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce babu wata niyya da yake da ita ta sauya sheka zuwa wata jam’iyya. Ya bayyana haka ne a taron NEC na jam’iyyar a Abuja.
6. ASUP ta bai wa Gwamnati kwana 21 ta warware matsalolin makarantu
Ƙungiyar malamai ta ASUP ta ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 don magance matsalolin da ke addabar ilimin kwalejin kimiyya da fasaha a ƙasar.
7. Gwamnati ta lalata bindigogi 13,000 cikin shekaru 4
Cibiyar kula da yaduwar ƙananan makamai ta ƙasa (NCCSALW) ta ce ta lalata bindigogi sama da 13,000 a cikin shekaru hudu domin rage yaduwar makamai a Najeriya.
8. Rikici tsakanin ’yan sanda da Civil Defence a Ebonyi, an kashe ɗan sanda
Wani rikici ya barke tsakanin jami’an ’yan sanda da na Civil Defence a ƙaramar hukumar Ivo, Jihar Ebonyi. An kashe ɗan sanda yayin da wasu suka jikkata.
9. Kuɗin fasfo ɗin Najeriya ya tashi daga N50,000 zuwa N100,000
Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta sanar da karin farashin fasfo. Fasfo na shekara 5, shafi 32, yanzu zai kasance N100,000; yayin da na shekara 10, shafi 64, ya tashi daga N100,000 zuwa N200,000.
10. ’Yan sanda sun rufe ofishin NLC a Edo
Jami’an ’yan sanda sun mamaye kuma suka rufe sakatariyar NLC a Jihar Edo, wacce aka fi sani da Adams Oshiomhole Labour House. Haka kuma, ƙofar makarantar UNIBEN an tsaurara tsaro tare da bayyanar wasu matasa da ake zargi da ’yan daba a wajen.