LABARAI NA YAU A NAJERIYA (30 GA YULI, 2025)
SHUGABA TINUBU YA NADA SABON SHUGABAN HUKUMAR KASHE GOBARA
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon Controller-General na Federal Fire Service (FFS). Sanarwar nadin ta fito daga babban sakataren hukumar kula da tsaro da gyaran hali, Janar Abdulmalik Jibril (rtd).
SHUGABA TINUBU YA GANA DA WANI AMINI NA KWANKWASO
A fadar shugaban kasa, Tinubu ya gana a boye da Hon. Abdulmumin Jibrin, dan majalisa kuma amintaccen Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Ganawar na iya danganta da yunkurin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da wasu bangarorin hamayya.
DSS TA SAKI WASU DA AKE ZARGI DA HANNU A KISAN MAKIYAYA
Hukumar DSS ta saki mutum uku da ake zargin suna da alaka da IPOB da kuma kisan makiyaya bakwai. Haka zalika, hukumar tana duba fiye da shari’o’i 20 na wadanda ake zargin an tsare su ba tare da hujja ba.
GWAMNA HYACINTH ALIA NA BENUE YA RUSA MAJALISAR ZARTASWA
Gwamnan jihar Benue ya rusa kwamitin zartarwa na jihar, sai dai ya nada Barr. Moses Atagher – tsohon kwamishinan shari’a – a matsayin Chief of Staff dinsa.
NNPC TA MUSANTA SAYAR DA MATATUN MAI
Kamfanin NNPC ya ce ba zai sayar da matatun man da ke hannunsa ba, ciki har da na Port Harcourt. Shugaban kamfanin, Bashir Bayo Ojulari, ya bayyana cewa aikin gyaran matatun zai ci gaba ne, ba a shirin raba su ga masu zaman kansu ba.
PETER OBI BAI SHIGA JAM’IYYAR ADC BA – INJI BOLAJI ABDULLAHI
Mai magana da yawun rikon kwarya na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa Peter Obi bai shiga jam’iyyar su ba tukuna, kodayake yana daga cikin kungiyoyin hadin gwiwar hamayya.
RUWAN SAMA YA RUSA GINE-GINE A MAIDUGURI
Gidaje takwas sun rushe sakamakon ruwan sama mai karfi da aka tafka a safiyar Laraba a Maiduguri. Gidaje da dama da ke yankunan Bulumkutu, Abuja, Moduganari da Ngomari sun lalace, yayin da iyalai da dama suka rasa matsugunai.
TSOHON DAN MAJALISAR JIHAR LAGOS, VICTOR AKANDE, YA RASU
Lauya kuma tsohon dan majalisar jihar Lagos, Hon. Victor Akande, ya mutu sakamakon hadarin mota da ya faru a karshen mako a Ojo. Ya rasu ranar Laraba, 30 ga Yuli, 2025.
FADAR SHUGABAN KASA TA MUSANTA ZARGIN CIN HANCI DAGA ADC
Mai magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala, ya karyata zargin Ralph Nwosu na cewa an ba shi mukaman ministoci uku don ya janye daga shirin hadin gwiwar hamayya. Bwala ya ce wannan “ƙarya ce marar tushe”.
’YAN GUDUN HIJIRA SUN TOSHE HANYA A BENUE–NASARAWA
’Yan gudun hijira daga Yelwata sun toshe babbar hanyar Benue–Nasarawa, suna zanga-zanga kan bukatar a mayar da su gidajensu. Sun dade suna fuskantar hare-hare daga makiyaya, kuma sun bukaci gwamnatin tarayya ta kawo musu mafita.