Labaran Najeriya Na Yau – 18 Ga Satumba, 2025
1. Tinubu Ya Cire Dokar Ta-Baci a Jihar Rivers
Shugaba Bola Tinubu ya cire dokar ta-baci daga jihar Rivers daga daren Laraba. Ya umarci Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da ‘yan majalisar dokokin jihar su koma bakin aiki daga Alhamis.
2. NECO Ta Kama Makarantu 38 da Sun Yi Cheeting
Hukumar NECO ta bayyana cewa makarantu 38 a jihohi 13 sun tafka rashin gaskiya baki ɗaya a jarrabawar SSCE ta 2025. An kuma bada shawarar a soke lasisin wasu masu sa ido 9.
3. FAAC Ta Rabawa Jihohi Naira Tiriliyan 2.225
Kwamitin Rabon Kuɗin Tarayya (FAAC) ya raba Naira tiriliyan 2.225 a watan Agusta 2025, mafi girma a tarihin rabon kuɗin tarayya.
4. Gobarar Lagos Ta Kashe Ma’aikatan FIRS Hudu
Hukumar FIRS ta tabbatar da mutuwar manyan ma’aikatanta hudu a gobarar Afriland Towers da ta tashi a Lagos ranar Talata.
5. Ɗan Damfara Da Ya Yi Kamar Soja An Kama Shi a Neja
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja ta kama wani da ya yi kamar soja domin ya saci babura a Minna. An kuma cafke wani a Bangi da ya saci babur.
6. Tarihin Najeriya An Mayar Da Shi Dole a Makarantu
Gwamnatin Tarayya ta dawo da darasin Tarihin Najeriya a matsayin darasi na dole a makarantun firamare da sakandare.
7. Ƴan Sanda Sun Kama Babban Ɗan Fashi a Delta
Ƴan sanda a jihar Delta sun cafke Emmanuel Emiowor, ɗan fashin da aka fi nema a jihar, wanda ke kai hari kan coci-coci da dare.
8. Najeriya Ta Shigo da Ton Miliyan 560 na Sinadarin Takin Zamani
Ma’aikatar Harkokin Kuɗi ta bayyana cewa Najeriya ta shigo da ton sama da dubu 560 na kayan haɗin taki a shekarar 2025 domin tallafa wa manoma.
9. Naira Ta Kara Faduwa
Naira ta fadi zuwa N1,537 kan kowanne Dalar Amurka a kasuwar bayan fage, yayin da ta fadi zuwa N1,498 a kasuwar NFEM ranar Laraba.
10. Saudiyya Ta Saki Mahajjata Ƴan Najeriya Uku
Hukumomin Saudiyya sun saki ƴan Najeriya uku da aka tsare a Jeddah bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi bayan sun shafe makonni hudu a tsare.