Labaran Najeriya Na Yau – 16 Ga Oct, 2025
1. Majalisar Dattawa za ta fara tantance Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, a yau Alhamis, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC). Daraktan bayanai na Ofishin Sakatare na Majalisar Dokoki, Bullah Audu Bi-Allah, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa ranar Laraba.
2. Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya yi murabus daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP). Kakakinsa, Daniel Alabrah, ne ya bayyana hakan, amma bai fayyace dalilin ficewarsa daga jam’iyyar ba.
3. Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce gwamnoni na jam’iyyar PDP da suka koma jam’iyyar APC ya kamata su gode masa. Wike ya ce kyawawan ayyukansa ne suka ba su damar yin hakan, kuma hakan ya tabbatar da goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu.
4. Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama wasu tsoffin jami’anta da aka kora, bisa zargin amfani da sunan hukumar wajen aikata zamba. Hukumar ta bayyana hakan a wata sanarwa ranar Laraba, inda ta ce waɗanda aka kama—Barry Donald da Victor Godwin—za a gurfanar da su a kotu.
5. Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa canjin jam’iyya da wasu gwamnoni suka yi zuwa APC ya tabbatar da matsayar da hadakar jam’iyyun adawa suka dauka cewa ana ƙoƙarin maida Najeriya jam’iyya ɗaya. A wata sanarwa, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyarsu ba ta damu da abin da ya kira “rashin aminci na siyasa” daga gwamnoni ba.
6. Sanata Seriake Dickson, wanda ke wakiltar Bayelsa ta Yamma, ya bayyana adawarsa ga yawaitar ficewar ‘yan siyasa zuwa jam’iyyar APC. Yayin da yake magana da ‘yan jarida a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a Abuja ranar Laraba, bayan zaman majalisa, Dickson ya ce yana nan daram a PDP.
7. Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya koka da yadda aka bar manyan ayyukan da ya fara lokacin da yake Gwamnan Jihar Bayelsa, yana zargin gwamnatocin da suka biyo baya da rashin ci gaba da tsare-tsarensa na cigaba. Yayin kaddamar da otal ɗin Best Western Plus Hotel a Yenagoa ranar Laraba, Jonathan ya ce ya fara gina wasu otal-otal domin jawo zuba jari da yawon bude ido a jihar kafin ya zama mataimakin shugaban ƙasa a 2007.
8. Babbar Kotun Jihar Kano, ƙarƙashin mai shari’a Musa Dahuru Muhammad, ta yanke wa wani kocin ƙwallon ƙafa, Hayatu Muhammad, hukuncin ɗaurin shekaru takwas a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba, saboda yin lalata da ƙaramin ɗan wasansa. An tabbatar da cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata laifin sau biyu a wurare daban-daban a yankin Dala.
9. Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce ta ceto mutane uku da aka sace tare da kama mutane shida da ake zargi da hannu a satar, a ƙauyen Euga, ƙaramar hukumar Toro ta jihar. Mai magana da yawun rundunar, Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
10. Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana a ranar Laraba cewa ya ƙi karɓar mukamin gwamnati daga Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa yanzu yana son mayar da hankali kan rayuwarsa ta kashin kai bayan shekaru da dama a harkar siyasa. Fayose, wanda mamba ne na jam’iyyar PDP, ya ce duk da dangantakar sa ta kusa da Shugaba Tinubu, ba shi da niyyar shiga ko karɓar wani mukami a ƙarƙashin gwamnatin APC.