Takaitattun Labaran Juma’a
Kwastam ta kama kayan fasa kwauri da kudinsu ya kai miliyan 78.6 a jihar Kebbi.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayar da gudunmawar tan 400 na kayan abinci ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno.
Tinubu ya ce matsalar ambaliyar ruwa za ta zama tarihi a Jihar Kogi muddin ya zama Shugaban Kasa.
Wasu mutum biyu sun mutu yayin da wani abu da aka binne ya fashe ya kuma tashi da su a Karamar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya NDLEA Buba Marwa, ya ce, hukumar na bukatar karin kwararrun karnukan farauta da ke shinshino boyayyun kwayoyi.
Red Cross ta kaddamar da shirin taimakawa wadanda ambaliya ta shafa a Najeriya.
‘Yan sintiri sun harbe ‘yan bindiga biyu bayan sun kai hari a kasuwar Gidan Goga da ke Karamar Hukumar Maradun a Jihar Zamafara.
An fara gudanar da bincike game da cin zarafin wani dan Jarida da man majalisar yayi.
Shugaban Equatorial Guinea ya kaddamar da takarar neman wa’adi na shida.
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Gerrard Pique, ya ce wasan da kungiyarsa za ta yi da Almeria a ranar Asabar shi ne wasansa na karshe a filin wasa na Camp Nou.
Europa League: Manchester United ta sami nasara akan Real Sociedad da ci 1:0 a wasan jiya.
Europa League: Arsenal ta sami nasara akan FC Zurich da ci 1:0 a wasan jiya.