SUNAYE: Mutum 10 da suka cinye jarabawar JAMB a bana, 2021

Hukumar shirya Jarabawar shiga jami’o’in Najeriya JAMB ta gabatar da sakamakon dalibai 10 da suka fi cin jarabawar shuga jami’o’in da aka rubuta a bana, 2021.

Shugaban hukumar jarrabawar, Ishaq Oloyede, ya gabatar da sakamakon daliban ne a taron musayen ra’ayoyi wanda ya samu halartar shugabannin jami’o’i da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi a kasar nan.

Ya ce dalibi na farko cikin jerin daliban shine Monwuba Chibuzor Chibuikem, namiji, mai lambar rajista, 10054281ID, daga jihar Legas.

Chibuikem ya zana jarabawar a jihar Legas kuma ya samu maki 358 daga cikin maki 400.

Na biyu shine Qomarudeen Abdulwasiu Alabi da Adeogun Kehinde Oreoluwa da suka samu maki 350. 

Alabi, dan asalin jihar Osun ne, mai lamba 10115691FG kuma ya zana jarabawar a jihar sa ta asali ne.

Oreoluwa, shima namiji ne, mai lamba 10109964GI, dan asalin jihar Ogun ne wanda ya zana jarabawarsa a jihar.

Na hudu shine Ajayi Eberechukwu Isaiah, namiji, mai lamba 10067858JC ya samu maki 349.

Isaiah Dan asalin jihar Legas ne ya zana jarabawar kuma a Legas.

Na biyar kuma mace ta farko a jerin sunayen wadanda suka yi nasara a jarabawar itace Favor Kenneth mai lamba 10088418AH daga jihar Ribas kuma ta rubuta jarabawa a jihar.

Favor ta ci maki 348.

Sauran daliban sun hada da Omonona Oluwamayokun Victor mai lambar rajista 10008972BG; Owoeye Israel Oluwatimilehin mai lamba 10165579GD, da Ehizogie Jeffrey Aidelogie mai lamba 10006469FG su ne na shida Kuma duk sun samu maki 347.

Na Tara shine Ajeigbe Moyinoluwa Samuel, mai lamba 10151081AE, namiji, daga jihar Ekiti. 

Moyinoluwa ya zana jarabawar a jihar Kwara kuma ya samu maki 346.

Yakubu Abdulraheem Joshua mai lamba 10050994FA, namiji, daga jihar Edo, ya zana jarabawar a Edo.
Joshua ya samu maki 343.

Jami’ar da dalibai suka fi zaba a bana

Oloyede ya ce dalibai biyar daga cikin 10 din da suka fi samun maki maiyawa a jarabawar sun zabi Jami’ar ‘Convenant’ dake Ota, Jihar Ogun.

Shugaban cocin ‘Living Faith’ David Oyedepo ne ya kafa Jami’ar.

Alabi wanda ya zo na biyu ya zabi jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) dake Ile-Ife sannan Oreoluwa ya zabi shiga jami’ar Legas.

Isiah, wanda ke matsayi na hudu ya zabi Jami’ar (FUNAAB), Jihar Ogun, Aidelogie ya zaɓi Jami’ar Afe Babalola, Ado-Ekiti (ABUAD), Jihar Ekiti.

Joshua ya zabi jami’ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK), Awka, jihar Anambra.

Darussan da daliban suka zaba.

Dalibai 8 daga cikin 10 sun zaɓi darussan kimiyya da injiniya.

Daya ya zabi darasin lissafi daya kuma ya zabi nazarin kimiyyar kwamfuta.