SUG: Dalibai sun ba Gwamnatin Tarayya da ASUU mako 1 su kawo karshen yajin-aiki
Kungiyar SUG ta bukaci Malaman Jami’a suyi sulhu da Gwamnatin Tarayya An shafe watanni kusan takwas ana fama da yajin-aiki a jami’o’in kasar nan – Shugabannin ‘Dalibai sun ce zasu yi ta zanga-zanga idan har ba a dawo aiki ba Wata kungiya ta shugabannin daliban jami’o’in da ke Arewacin Najeriya ta bada wa’adin mako guda ga ASUU da gwamnatin tarayya a kan yajin-aiki. Shugabannin na SUG sun ce za su barke da zanga-zanga a kasar, muddin lokacin da su ka bada ya wuce ba tare da yajin-aikin da ake yi ya zo karshe ba. Jaridar Vanguard ta ce ‘yan kungiyar na SUG sun bayyana wannan ne a wani taro da su ka shirya ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, 2020, a garin Kano.
A wajen wannan taro, shugaban tafiyar, Sadi Garba Sa’id daga jami’ar Bayero ta Kano, ya karanto matsayar da suka cinma a zaman da su kayi a Jigawa. Ya ce: “Kungiyar ta amince ta sake duba bukatan ASUU. Gamayyar ta na ba duka bangarorin mako guda da nufin su shawo kan sabanin da ke tsakaninsu.” Mista Garba Sa’id ya ke cewa: “Idan ba ayi haka ba, daliban Najeriya za su hau kan tituna, mu dauki darasi a can.” A cewar Sa’id, SUG ba za su amince da karin kudin makaranta ba, har ma ya yi kira ga gwamnati ta biya kudin makarantar yara saboda halin da aka shiga.
“A duba lamarin shekarun zuwa NYSC domin akwai yiwuwar yajin-aikin ASUU da yaki zuwa karshe ya shafi shekarun daliban da ke shirin bautar kasa.” Har ila yau, kungiyar shugabannin daliban ta roki gwamnati ta shigo da tsare-tsaren koya wa dalibai sanin bakin aiki da sana’o’in da za su rike kansu. Adamu Adamu ya ce alkawarin da aka yi wa Jami’o’i a baya ya jawo matsala. A cewarsa, bai kamata Gwamnatin baya ta shiga yarjejeniyar N1.3tr da ASUU ba. Ministan ilmi ya yi alkawarin cewa kwanan nan malaman makarantar za su koma bakin aiki.