Site icon TWINS EMPIRE

Soke Bukin Zagayowar ’Yancin Kai Na Nuna Rabuwa Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da ’Yan Najeriya – ADC

Kakakin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC)Bolaji Abdullahi, ya soki matakin gwamnatin tarayya na soke bukin Zagayowar Cikar Shekaru 65 da samun ’Yancin Kai da aka shirya gudanarwa a Abuja ranar 1 ga Oktoba, yana mai cewa wannan alama ce ta yadda fadar shugaban kasa ta rabu da talakawan Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta sanar a ranar Litinin cewa ba za a yi bukin taron faretin ba, duk da cewa sauran shagulgulan bikin za su gudana kamar yadda aka tsara.

A cikin hirar da ya yi da DAILY POST a ranar Talata, Abdullahi ya bayyana cewa wannan biki na faretin wata alama ce mai muhimmanci da bai kamata a watsar da shi ba.

Ya ce: “Bikin ’yancin kai babban lokaci ne da ke karfafa gwiwar ’yan kasa, da kuma nuna kyakkyawan hoton Najeriya a idon duniya. Don me aka soke shi kwatsam?”

Ya yi zargin cewa babban dalilin sokewar shi ne rashin kasancewar Shugaba Bola Tinubu a Abuja, maimakon matsalolin tattalin arziki da gwamnati ta bayyana.

Abdullahi ya kuma zargi gwamnati da rashin daidaito, inda ya ce an riga an aika da gayyata tun kafin a fuskanci matsin tattalin arziki, amma daga baya aka yi hujja da shi.

Har ila yau, ya soki rashin halartar Shugaba Tinubu a wasu manyan taruka na kasa, musamman bikin kammala horon sojoji na makarantar koyon dabarun soja ta NDA, inda aka nada sabbin sojoji sama da 800 a karshen mako.

“Idan shugaban kasa ba zai iya halarta da kansa ba, ya kamata aƙalla ya tura Babban Hafsan Soja. Amma sai aka ji shi yana Legas, yana kaddamar da sabunta Gidan wasan kwaikwayo na kasa,” in ji shi.

A cewarsa, irin wannan matakai na rage darajar Najeriya kuma suna nuna rashin fifikon abubuwan da suka shafi ci gaban kasa.

Exit mobile version