Sojojin Najeriya Sun Kama Wasu ‘Yan Bindiga Na Kasashen Ketare
Hedkwatar tsaron Najeriya tace dakarunta na Operation Hadarin Daji
dake aikin kakkabe yan ta’adda a yankin arewa maso yammacin Najeriya
sun cafke wasu yan ta’addan kasashen waje dake hada kai da na Najeriya
wajen tafka aika aika,
Daraktan cibiyar tattara bayanai a Hedkwatar tsaron Kasar kan
arangamar da dakarun kasar keyi Manjo Janar Bearnad Onyeako yace an
cafke yan bindigar ne a dajin dake cikin yankin karamar hukumar Jibia
a Jihar Katsina.
Janaral Onyeako wanda yaki yin bayanin ko daga wacce kasa yan
bindigar suka fito yace sanin ko daga ina mutanen suka fito ba shi ne
mai muhimmanci ba, amma irin gagarumin kokarin da dakarun kasar sukai
na gano da cafke yan bindigar shine abin lura.
Kamar yadda VOA ta wallafa cewa A dai wannan mako ne wasu yan bindiga suka bindige wani malami a wata
mata makarantar sakandare dake jihar Nasarawa, Al’amarin kuma dake
zuwa daidai lokacin da sufeta Janar na Yansandan kasar ke bada umarnin
kara tsaurara tsaro a baki dayan makarantun kasar.
Kamar yadda masanin tsaro Salihu Othman Dantata ke cewa wannan umarnin
yayi daidai inda yake ganin bama Yansanda kadai ba, akwai bukatar ayi
hadaka da sauran jami’an tsaro irin na DSS da Civil Defence don
tabbatar da samar da cikakken tsaro a baki dayan makarantun kasar.
Salihu Dantata yace a duk lokacin da yan ta’adda suka gaza cimma wani
babban wurin da zai kassara gwamnati to suna maida hankakaline kan
makarantu don jan hankalin duniya akansu.