Sojoji sun gano haramtattun matatun mai 50 a Neja Delta
Rundunar sojin Najeriya ta bankaɗo haramtattun matatun mai 50 a dajin Biseni da ke ƙaramar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa, a Neja Delta mai arzikin man.
Kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Operation Delta Safe a yankin Neja Delta, Rear Admiral John Okeke wanda kuma ya jagoranci samamen ne ya bayyana haka.
Okeke wanda yake magana da ƴan jarida ya ce a ranar 9 ga watan Mayu, sun kai samame ƙaramar hukumar Ukwa ta Yamma da ke jihar Abia kan iyaka da Rivers, ya kuma ce za su ci gaba da kai irin wannan samame domin gano wasu matatun mai da ake gudanar da su ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa, sun gano wani rami da aka haƙa a ɗaya daga cikin haramtattun matatar mai wanda ke iya ɗaukan manyan motoci 10 maƙare da duro-duro na iskar gas inda kuma suke ajiye ɗanyan mai wanda daga nan kuma su riƙa shigar da shi wurin girke-girkensu.
Rear Admiral John Okeke ya ƙara da cewa za su ci gaba da kai irin wannan samame domin fatattakar masu fasa-ƙwabrin mai a yankin na Neja Delta.