Shugaban Gwamnatin Jamus Ya yi Ratse A Nijer
Bayan da ya je kasar Senegal, Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya isa birnin Yamai na Nijer inda ya gana da shugaba Mohamed Bazoum da mukarraban gwamnatinsa kafin ya ziyarci sojojin Jamus da ke aiyukan bada horo a karkashin rundunar hadin guiwar nahiyar Turai da ake kira La Gazelle.
Ziyarar wacce ke gudana watanni kadan bayan da aka zabi Olaf Scholz a matsayin shugaban gwamnatin Jamus na hangen jaddada matsayin kasar a yaki da kungiyoyin ta’addancin yankin Sahel. Ya kuma fara ne da gundumar Tilia, inda sojojin Jamus na musamman da ake kira Forces Speciales ke gudanar da aikin bada horo ga dakarun tsaron Nijer.
“Jamus da Nijer na da kyaukyawar huldar aikin tsaro da ake kira Mission Gazelle, na ziyarci inda aiyuka ke gudana na ganewa idanuwana na kuma lura da yadda ake samun nasarorin. Hulda ce ta gaskiya, dalili kenan ake samun kyawawan sakamako,” a cewar Scholz.
A watan Disamban da ke tafe ne sojojin Jamus masu sansanin bada horon soja a Tilia ke kammala aiki saboda haka shugaban Nijer Mohamed Bazoum ya bukaci kasar ta Jamus ta tsawaita wannan aiki.
Ya ce wannan abu ne da sojojin kasar Nijer ke dauka da matukar muhimmanci saboda haka na bukaci a kara bamu damar morar horon nan da dakarunmu ke ganin ya kamata dukkan kasashe aminai su yi koyi da shi.
Shugaban kasar ta Nijer ya kuma bukaci kasar Jamus ta kara yawan tallafin da take bai wa Nijer a fannin ilimi, musamman abinda ya shafi makarantun koyon sana’oin hannu.
Ya kuma ce manyan kalubalen da suka haddasa talauci a Nijer abubuwa ne da ke da nasaba da batun ilimi, saboda yadda yawan yaran da ake haifa ke fin karfin tsarin karantarwa sannan na bukaci Jamus ta bamu gudunmowa a aiyukan gina makarantun kwanan ‘yan mata da muka sa gaba.
Olaf Scholz ya tabbatar da cewa kasarsa ta amince ta bai wa Nijer gudunmowar da take bukata a fannonin da kasashen biyu ke da dadaddiyar hulda ta tsawon shekaru a kalla 61.
Nan gaba majalisar dokokin kasar za ta tattauna wannan bukata don yin na’am da ita.
Batun karfafa dimokradiyya, da shimfida mulki nagari, da maganar sakin ragama ga kananan hukumomi, da batun zaman lafiya da inganta sha’anin noma na daga cikin fannonin da Jamus ke tallafa wa Nijer.
Olaf Scholz zai Karkare wannan rangadi da Afrika ta kudu a ranakun Talata 24 da Laraba 25 ga watan mayu.