Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya isa Jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar a ranar Alhamis
Me Shugaba Buhari zai je yi Jihar Imo, cibiyar kungiyar IPOB?

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya isa Jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar a ranar Alhamis, ɗaya daga cikin jihohin da masu fafutukar kafa Biafra ke neman ɓallewa.
Ya yi tafiyar ne a wata ziyarar aiki don kaddamar da wasu ayyuka.
Rahotanni daga jihar Imo na cewa ƙungiyar ta ba da umarnin jama’a su zauna a gida a ranar Alhamis din saɓanin Litinin, wani abu da ake ganin yana da nasaba da ziyarar ta Shugaba Buhari.
Wannan ziyara ita ce ta farko da shugaban zai yi tun bayan da ‘yan kungiyar Ipob suka zafafa kai hare-hare a kwanakin baya kan jami’an tsaro da gine-ginen gwamnati, a fafautukar da suke yi ta ballewa daga kasar.
A baya-bayan nan kungiyar ta umarci al’ummar yankin kudu maso gabashin Najeriya da su dinga zama a gida duk ranar Litinin don nuna turjiya ga mahukunta da kuma jawo hankalin gwamnati ta saki jagoransu Nnamdi Kanu.
Amma saboda wannan ziyara da shugaban zai yi, sai Ipob ta umarci al’ummar yankin da cewa kar wanda ya fita, don nuna wa shugaban karfin ikon da kungiyar ke da shi a yankin.
Sai dai gwamnatin jihar Imo din ta gargadin yan kungiyar ipon da su janye jiki yayin ziyarar, kmaar yadda kwamishinan yada labaran jihar ya fitar a ranar Laraba.
Sannan gwamnati ta yi wa ‘yan jihar umarni su yi watsi da batun Ipob, tare da cewa ta shirya tsaf don tarbar shugaban kasa, kuma jama’a suna dokin tarbar shugaban kasar.
Wadanne ayyuka Shugaba Buhari zai kaddamar?
Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu manyan ayyukan da Gwamna Hope Uzodimma ya yi, a cewar mai magana da yawun gwamnan.
Babban jami’in yada labarai na gwamnan Oguwike Nwachukwu, ya ce ziyarar za kuma ta nuna cewa gwamnatin tarayya na son ci gaban jihar Imo.
A cewar Nwachuckwu, ayyukan da Shugaba Buhari zai kaddamar sun hada da:
- Manyan magudanan ruwa na karkashin kasa na zamani – Chukwuka Nwoha
- Titin Naze/ Nekede/Ihiagwa
- Titin Egbeada By-Pass – Amakohia
- Sabon gini na majalisar zartarwa da ke cikin iidan gwamnatin jihar wato Douglas House.
