Sharuddan Da Twitter Ta Cika

Mnistan yada labarai Lai Mohammed ya ce Twitter yana tara makudan kudade daga Najeriya ba tare da goyon bayan doka ko bin dokokin kasar ba.

Kamfanin sada zumunta na Twitter ya samu ‘yancin gudanar da ayyukan sa a Najeriya domin ya cika sharruda 6 da Gwamnatin Najeriya ta gindaya masa.

Sai dai kwararru a fannin kimiya da fasaha na cewa ba karamin hasara bangarorin biyu suka tafka ba cikin watani 7 da aka dakatar da kamfanin a bisa zargin su da laifin cire wani sako da Shugaba Mohammadu Buhari ya wallafa a shafin sa na twitter.

Shugaban Kasa Mohammadu Buhari ya amince da dage takunkunmin ne bayan shawarar da shugaban Kwamiti na musamman da Gwamnati ta nada Kashifu Inuwa Abdullahi ya bayar.

Wannan ci gaban yana nufin yawancin ‘yan Najeriya na iya dawowa da amfani da dandalin sada zumunta na Twitter bayan watanni 7 da rufe shi. 

Bincike ya nuna cewa Kamfanin Twitter ya cika sharrudan da Gwamnati ta gindaya masa wanda ya hada da bude Ofishin su a Najeriya a karkashin wakili da zai gudanar da ayyukan su.

Kazalika ya yi rajista da Hukumar Harkokin Kasuwanci wato CAC, samun lasisin Hukumar Watsa labarai ta Kasa da biyan haraji kuma ba a yarda Twitter ya yi katsalandan a harkar tsaron kasa ta watsa labaran karya ko cin zarafi ba.

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya ce Twitter yana tara makudan kudade daga Najeriya ba tare da goyon bayan doka ko bin dokokin kasar ba.

An yi hasashen cewa ‘yan Najeriya sun yi hasarar sama da Naira biliyan 6 a watanni 7 da aka haramta amfina da shi a kasar, ita ma Gwamnatin kasar ta yi hasarar kudade da yawa in ji masanin tattalin arziki Abubakar Ali.

Bangarorin biyu, wato Twitter da Gwamnatin Tarayya sun cimma matsaya kan yadda za a rika bayar da rahoton munanan kalamai ko rahotanni da ke kawo cikas ga tsaron kasa, wani abu da kwararre a fannin sadarwa kuma mai amfani da dandalin Twitter Auwalu Abdullahi ya ce matakin da aka dauka ya taimaka wajen gyara abubuwa da suka faru a baya.

A lokacin warware wannan takaddama, alamu sun nuna cewa Gwamnati na haraman yi wa dokar Hukumar Kula da Kafofin yada labarai NBC kwaskwarima da za ta hada da Facebook, Instagram, WhatsApp da sauran kafafen sada zumunta.