Saura kwana 3 daurin aure, uwargida ta kashe budurwar mijinta
‘Yan sanda jihar Kano sun cafke wata mata mai shekaru 20 da laifin kisan budurwar mijinta – Suwaiba ta kashe Aisha ana sauran kwana uku daurin aurenta da mijinta Malam Shahrehu – Suwaiba ta sanar da yadda ta ja Aisha wani kango sannan ta caka mata wuka a kirji, wuya da jiki Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata matar aure mai shekaru 20 mai suna Suwaiba Shuaibu a kan zarginta da sokawa wata Aisha Kabir wuka ana sauran kwanaki kadan aurenta.
An gano cewa Aisha ce wacce Malam Shahrehu Alhaji Ali, mijin wacce ake zargin zai aura a ranar 9 ga watan Janairu a kauyen Gimawa, karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, Daily Trust ta wallafa. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata, ya ce an nema amaryar an rasa amma daga baya sai aka ga gawarta a wani kango.
Kamar yadda takardar tace: “A ranar 2 ga watan Janairu wurin karfe 10:30 na safe mun samu labarain ganin gawar Aisha Kabir daga kauyen Gimawa a wani kango. “Mai korafin ya ce ana zargin an soka mata wuka ne a wuya. Mun ziyarci wurin inda muka dauka gawarta zuwa babban asibitin Tudun Wada wanda likita ya dubata.
“Kwamishinan ‘yan sanda CP Habu A. Sani ya bukaci jami’an tsaro da su nemo wadanda suka yi aika-aikar. “A wannan halin ne aka damko Suwaiba Shuaibu mai shekaru 20. Bincike ya nuna cewa mijinta ya kashe shekaru 6 suna soyayya da budurwar kuma za su yi aure.