Ziyarar ta Antony Blinken ta zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan yawan fararen hula da aka kashe a Gaza sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa.

Kafin tashinsa zuwa Tel Aviv, Blinken ya ce zai nemi “matakai na musamman” daga Isra’ila don tabbatar da cewa an rage cutar da fararen hula Falasdinawa, duk da cewa Amurka ta ki amincewa da kiran tsagaita bude wuta.

Mai magana da yawun fadar White House, John Kirby, ya ce Amurka ba ta bayar da shawarar tsagaita bude wuta ba ne, sai dai a dakatar da wani lokaci na wucin gadi.