Ruwan Sama Ya Cinye Yan Mata Biyu, Dabbobi Aƙalla 144, Tare da Rusa Gidaje da Dama a Sokoto

Ambaliyar ruwa sanadiyyar ruwa mai ƙarfi ya laƙume rayukan yan mata biyu tare da dabbobi sama da 140 Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ja’oje dake ƙaramar hukumar Wamakko, inda gidaje dama suka rushe Shugaban sashin jin ƙai na hukumar SEMA ya ce akwai sauran ƙauyuka biyu da abun ya shafa Wasu yan mata biyu kuma yan uwan juna sun rasa rayuwarsu sanadiyyar ambaliyar ruwa a ƙauyen Ja’oje dake ƙaramar hukumar Wamakko, jihar Sokoto, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Hamida da Maryam sun rasa rayuwarsu ne bayan ɗakin da suke bacci ya faɗa musu sanadiyyar tsananin ruwan sama da ake yi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban sashen jin ƙai na na hukumar bada taimakon gaggawa (SEMA), Mustapha Umar, ya bayyana cewa ambaliyar ta laƙume dabbobi aƙalla 144.

Umar ya ƙara da cewa ambaliyar ta shafi gidaje da dama, domin lamarin ya shafi magidanta kimanin 177. Yace: “Haɗakar jami’an hukumar bada agaji ta jihar Sokoto (SEMA), hukumar ta ƙasa (NEMA), da kuma wasu ƙungiyoyi sun dira ƙauyen domin duba irin asarar da aka yi.”