Rundunar Tsaro Ta Nigeria Ta Magantu Kan Seaman Abbas

Rundunar Tsaro Ta Nigeria Ta Magantu Kan Seaman Abbas

Hedikwatar Tsaro ta ce ta fara bincike kan zargin wanda ya tayar da ƙura da jawo mata suka sa zargin tauye haƙƙi a faɗin ƙasar.

Karamin Ministan Tsaro, Matawalle, ta hannun kakakinsa, Ahmed Dan-Wudil, ya ce binciken ya zama dole, domin wajibi a mutunta tare da kare haƙƙin kowane soja, komai kankantan matsayinsa.

Tuni da ma, Ƙungiyar Dattawan Arewa ta bukaci, Babban Hafsan Tsaron, Janar Christopher Musa, ya gaggauta bincikar zargin tsare sojan mai muƙamin Seaman, tsawon shekaru shida, har sai da ya samu tabin hankali a yayin da ake tsare da shi.

Hakan na zuwa ne bayan matar Seaman Haruna Abbas ta kai kara bisa yadda kwamandan bataliyansa, Muhammad S. Adamu, ya sa aka tsare mijin nata ba bisa ka’ida ba tsawon shekara shida, har mijin nata ya samu tabin hankali.

A cikin bidiyon, wanda aka naɗa daga shirin ‘Brekete Family’ na gidan rediyo da talabijin na Human Rights, an ga matar Seaman Abbas tana zayyana yadda mijin nata ya shafe shekaru a tsare, har sai da ya samun tabin hankali.

An ji tana bayyana wa mai gabatar da shirin cewa a sakamakon sabanin da mijin nata ya samu da kwamandan bataliyansa kan yin Sallah ne ya sa aka tsare Seaman Abbas.

A cewarta, lamarin ya kai ga har sai da mijin tana ya zauce a tsare, kuma ita ce ke saya wa masa magani a inda ake tsare da shi, kafin daga bisani sojoji su kai shi asibiti.

Bayan nan kuma suka sake dawo da shi aka tsare shi, har sai da lalurar ta sake dawowa.

Matar Seaman Abbas Haruna mai suna Hussaina, ta bayyana cewa duk ƙoƙarinta na ganin an sako mijin nata ya gagara, duk kuwa da shekaru da kwashe tana kai-komo da rokon wadanda take zaton za su iya sanya baki a gidan sojin.

Ta bayyana cewa, ko a lokacin da aka ɗauki mijinta zuwa asibiti, sai da wasu da ba ta sani na suka rika kira suna mata barazana.

Wannan lamari dai ya jawo wa rundunar kakkausar suka daga bangarori daban-daban, tare da kira da a yi wa Seaman Abbas Haruna adalci.

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta hannun Daraktan Yaɗa Labaranta, Abdul-Azeez Suleiman, ta bukaci Hedikwatar Tsaro ta gaggauta ɗaukar mataki domin ƙwato haƙƙin Seaman Abbas Haruna da iyalinsa.

“Hakika bayanan da matar Abba ta yi a shirin ‘Brekete Family’ game da yadda ake tsare mijinta, suna da matukar tayar da hankali tare da sanya alamar tambaya kan batun adalci a aikin soji.” in ji sanarwa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, don haka “Muna kira ga shugabannin tsaron Najeriya su gaggauta duba lamarin Seaman Abbas Haruna da iyalansu da kuma yi masa magani.

“Wajibi ne a gaggauta magance wannan cin zalin da aka yi masa domin dawo da martabarsa da ta iyalinsa,” in ji sanarwar.

“Hakika bayanan da matar Abba ta yi a shirin ‘Brekete Family’ game da yadda ake tsare mijinta, suna da matukar tayar da hankali tare da sanya alamar tambaya kan batun adalci a aikin soji.”

A ranar Lahadi da bidiyon ya karfe gari ne Hedikwatar Tsaron ta sanar ta hannun Darektan yada labarai, Birgediya Janar Tukur Gusau, ta sanar cewa za a gudanar da bincike kan tsarewar da aka yi wa Seaman Abbas Haruna.