Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana samun nasarar cafke wani ƙasurgumi kuma gogarma a cikin kwamandojin Boko Haram.

An damƙe Yawi Modu kwanan nan a Barno, kuma dama ya na a jerin sahun farko na wasu riƙaƙƙun kwamandojin Boko Haram da sojoji su ka buga tandar cigiyar su ko da rai ko babu.

Cikin wata sanarwar da Kakakin Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, Burgediya Janar ɗin ya ƙara da cewa Sojojin Najeriya sun kuma kai farmaki a wata maɓuyar haɗa nakiya a Barno da Yobe.

Idan ba a manta shekaru biyar da su ka gabata sojojin Najeriya sun buga hotunan wasu riƙaƙƙun ‘yan Boko Haram fiye da su 100 da Hukumar Sojojin Najeriya ɗin ta ce ta na cigiya bakin rai, bakin fama.

An kama Modu ne a daidai lokacin da ɗaruruwan ƴan Boko Haram tare da iyalan su ke ci gaba da miƙa wuya su na saranda ga Sojojin Najeriya.

Nguyen

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga wata hira da ta yi da Babbar Jami’ar UNICEF da ke Maiduguri, Nguyen, wadda ta tabbatar wa wannan jarida cewa a cikin shekaru 11 Boko Haram sun kashe malaman makarantun Boko 2,295, kuma sun ragargaza makarantun Boko 1,400.

Boko Haram sun kashe malaman makaranta 2,295, sun ruguza makarantu 1,400 a Barno.

Hukumar Bunƙasa Ilmin Ƙananan Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ta bayyana takaicin yadda a cikin shekaru 12 Boko Haram su kashe malaman makarantun zamani har su 2,295 a Barno.

Cikin wata tattai musamman da ta yi da PREMIUM TIMES, Babbar Jam’iar UNICEF a Maiduguri, Phuong Nguyen ta kuma bayyana takaicin cewa tsakanin 2009 zuwa 2020 Boko Haram sun lalata makarantu 1,400 a Barno.

Nguyen wadda ta taɓa zama wakiliyar UNICEF a Somaliya, ta ce hare-haren ta’addanci sun matuƙar durƙusar da harkokin ilmi a Arewa maso Gabas na Najeriya, musamman a jihar Barno.

“An kulle dukkan makarantun Jihar Barno daga watan Disamba 2013 har zuwa Yuni 2015. Wannan ba ƙaramin koma-baya ba ne.

“Su ma jihohin Adamawa da Yobe sun fuskanci irin wannan matsala, an kulle makarantun ba su daɗe sosai kamar jihar Barno ba.”

Nguyen ta ce hare-haren dama kai-tsaye ana yin su ne domin a kassara harkar ilmi a jihohin, kuma sun yi mummunar illa wajen mayar da yankin, musamman jihar Barno koma-baya a ɓangaren ilmi.

Ta ce binciken baya-bayan nan da HNO ta yi ya nuna kashi 52% na ƙananan yaran jihar ba su taɓa zuwa makaranta ba.”

Nguyen ta ce dubban ɗaruruwan ƙananan yara na rayuwa maras tabbas a sansanonin masu gudun hijira, wasu babu iyaye, wasu kuma an tsallaka da su ƙasashe makwabta su na gudun hijira.

Ta nuna damuwar ta dangane da makomar yaran waɗanda ba su zuwa makaranta, musamman ma yara mata ƙanana.

Jami’ar ta UNICEF ta ce kisan malaman makaranta babban cikas ne wajen samar da ilmi, kuma wannan matsala ce ta ƙara haifar da taɓarɓarewar ilmi a yankin, musamman a jihar Barno.