Rundunar ƴan sandan Ghana ta sanar da cafke shahararren mawakin nan na ƙasar Shatta Wale
Rundunar ƴan sandan Ghana ta sanar da cafke shahararren mawakin nan na ƙasar Shatta Wale mai janyo ce-ce ku-ce da wasu mutum biyu, bayan ya yaɗa labarin ƙanzon kurege a shafin sada zumunta cewar wasu mutane biyu sun harbe shi.
Mawakin shi ne ya kai kansa wurin ƴan sanda bayan an bayyana shi a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo bayan ƙaryar harbin sa da ya yi
A cikin wata sanarwar da rundunar ƴan sandan ta Ghana ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce bayan sun bayyana Shata Wale da wasu mutum biyu yaransa a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo ne, mawakin ya miƙa kansa.
Sanarwar ta ƙara da cewa an cafke shi ne don ya taimaka wa ƴan sanda a binciken da suke yi an zargin sa da watsa labarin kanzon kuren mutuwarsa don tayar da zaune tsaye da jefa fargaba a zuƙatan jama’a.
Tun dai a wata sanarwar da rundunar ƴan sandan ta wallafa a baya ta yiw a al’umma gargadi da su daina yayata labaran ƙanzon kuregen da ka iya kawo tarnaƙi ga zaman lafiya ko a cafke mutum tare da hukunta shi.
Tun dai a watannin baya ne wani malamin kirista ya yi hasashen cewa za a kashe mawaki Shata Wale mai a ran 18 ga watan Oktobar wannan shekara.
A nasa bangaren mawakin ya ce ya watsa labarin ƙanzon kuregen cewa wasu mutane sun harbe shi a unguwar East Legon da ke birnin Acrra ne, saboda hukumomin tsaro sun gaza ba shi kariya, bayan hasashe wahayin mutuwar da malamin kiristan ya yi a kansa.
Sai dai tuni shi ma wannan malamin kiristan da ya yi harsahen wahayin ƴan sanda suka yi awon gaba da shi don taimaka wa wurin gudanar da bincike.
Al’umma dai sun fara jinjinawa sabon shugaban ƴan sanda George Akufoo wanda ake ganin ya fara aikinsa ba sani sabo inda wasu ma sun fara yi masa laƙabi cinnaka ba ka san na gida ba.
Yayin da da yawa suke cigaba da caccakar shaharren mawakin, wasu ma na ganin ya yi hakan ne don tallatar da sabon kundin wakarsa mai taken Gift of God wanda ake sa ran zai saka kwanan nan.
Sai dai da yawan mabiyansa na cigaaba da ɗaure masa gindi musamman a shafukan sada zumunta.
Yanzu abin jira a gani shi ne irin hukuncin da za a yanke akan wanda ake zargin.