Ronaldo Ya Amince da Kwangilar Saudiyya akan £173m
Cristiano Ronaldo ya amince da kwantiragin fam miliyan 173 a shekara da kungiyar Al Nassr a kasar Saudiyya, wanda zai sa ya zama dan wasan da ya fi samun kudin shiga a wasanni, in ji Daily Mail UK.
Dan wasan mai shekaru 37 a duniya an dakatar da kwantiraginsa na Manchester United a farkon wannan watan, biyo bayan takun saka tsakaninsa da shugabannin kungiyar.
Tauraron dan kwallon Portugal din a wata hira da yayi da Piers Morgan yayi kakkausar suka ga kungiyar Manchester United a matsayin kungiya da kuma kociyan kungiyar Erik Ten Hag, ya na mai cewa kungiyar bata girma tun bayan tafiyar Sir Alex Ferguson a shekarar 2013.
Ya kara da cewa ba ya mutunta Ten Hag saboda kocin ba ya girmama shi.
Sai dai wasu majiyoyi na kusa da tauraron sun dage cewa babu wata yarjejeniya da aka kulla, kuma Ronaldo ya ci gaba da maida hankali kan gasar cin kofin duniya da kasarsa, amma rahotanni a Spain a yau daga jaridar Spain, Marca ta ce an amince da alkaluman.
Sau biyar wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ya kawo karshen kwantiraginsa da Manchester United a ranar 22 ga watan Nuwamba bayan da kulob din ya gode wa tauraron dan wasan na Portugal saboda gudunmawar da ya bayar a wasanni biyu da ya zira kwallaye 145 a wasanni 346.