Sabon rikicin da ya sake ɓarkewa tsakanin Alhaji Aliko Dangote, Shugaban Kamfanin Dangote Refinery, da Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai na Midstream da Downstream ta Ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed, tare da masu shigo da man fetur da ‘yan kasuwa, ya jawo saukar farashin man fetur zuwa mafi ƙanƙanta a faɗin ƙasar.
A ranar Lahadi, Dangote ya yi jerin zarge-zarge kan shugaban NMDPRA, ciki har da kiran sa “mai lalata tattalin arziki”, bisa dalilin ƙarfafa shigo da man fetur duk da cewa matatar Dangote na da isasshen ƙarfin tacewa.
Attajirin ya kuma yi zargin cewa Farouk Ahmed ya kashe har dala miliyan 5, wato sama da Naira biliyan 7, wajen biyan kuɗin makarantar ‘ya’yansa a Switzerland. Sai dai hukumar NMDPRA ta musanta wannan zargi tun a watan Yulin 2025, tana mai cewa ƙarya ce.
An fara jin wannan zargi ne daga wata haɗakar ƙungiyoyin farar hula (CSOs) ƙarƙashin Lawyers in Defence of Good Governance.
Sai dai yayin da Dangote ya sake maimaita zargin a ranar Lahadi, ƙungiyar farar hular ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin ta bakin daraktanta, Olawale Mudasiru, inda ta janye zargin, tana mai cewa an yaudare su da bayanan ƙarya.
Ya ce:
“Zarge-zargen da muka yi tun farko sun dogara ne da bayanan da ba su da inganci. Daga baya mun gano cewa ‘ya’yan Injiniya Farouk Ahmed sun karanta ne da tallafin karatu, kuma sun kammala karatunsu tun kafin naɗinsa.”
Duk da haka, zargin ya riga ya jefa fargaba a tsakanin masu ruwa da tsaki a ɓangaren kasuwancin mai.
Sabon kalubalen da Dangote ya jefawa Ahmed ya biyo bayan rage farashin man fetur daga N828 zuwa N699 a kowace lita a tashar matatar sa, domin ya fitar da masu shigo da mai daga kasuwa, inda farashin su a ma’ajiyar ajiya (ex-depot) ya kai aƙalla N824 a makon da ya gabata.
Dangote ya bayyana a taron manema labarai na ranar Lahadi cewa bai kamata ‘yan Najeriya su sayi man fetur sama da N740 a kowace lita ba daga ranar Talata a watan Disamba da Janairu.
Ya sha alwashin amfani da dukkan dukiyarsa domin tabbatar da saukar farashin man fetur.
Masu ruwa da tsaki a harkar masana’antu sun bayyana hakan a matsayin dabara ta kasuwa da Dangote ke amfani da ita domin tilasta wa ‘yan kasuwa sayen man fetur daga matatar sa da kuma mamaye kasuwa.
Binciken Twins Empire ya nuna cewa tashar man Bovas da ke Wuse Zone 6 a Abuja ta rage farashin man fetur daga N910 zuwa N865 a kowace lita.
Haka zalika, Empire Energy da Ranoil da ke Gwarimpa, Abuja, sun daidaita farashin su zuwa N912 da N910 a kowace lita.
Kamfanin NIPCO da tashoshin AA Rano a Abuja na sayar da man fetur a N915, N905 da N910 a kowace lita zuwa daren Litinin.
Wani manajan tashar MRS, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya shaida wa DAILY POST cewa farashin man fetur ya tsaya a N910, amma akwai yiwuwar saukarsa daga ranar Talata.
Masu ajiya masu zaman kansu kamar Menj, Bovas, AA Rano da Integrated sun rage farashin su zuwa N710 daga kusan N824 a kowace lita.
Sai dai farashin ajiya na AYM Shafa, Raniol da wasu ya tsaya a N815 a kowace lita.
‘Yan kasuwa sun fara aiwatar da rage farashin mai a faɗin ƙasa – IPMAN
Mai magana da yawun Ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Najeriya (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya shaida wa DAILY POST cewa ‘yan Najeriya za su fara ganin rage farashin man fetur a tashoshin mai daga ranar Talata zuwa mako mai zuwa.
Ya ce:
“Daga ranar Talata da mako mai zuwa, za ku ga tasirin wannan rage farashi.”
Dangane da rikicin Dangote da Ahmed, ya ce ya dace ɓangarorin biyu su haɗa kai domin amfanin ‘yan Najeriya.
Rikicin Dangote da Ahmed ba zai amfanar da ‘yan Najeriya ba – PETROAN
Shugaban Ƙasa na Ƙungiyar Masu Tashoshin Sayar da Man Fetur ta Najeriya (PETROAN), Billy Gillis-Harry, ya musanta zargin cewa ana ƙoƙarin hana matatar Dangote aiki, yana mai kiran hakan “maganganu marasa tushe” da ke fitowa daga rikicin kasuwa.
Ya gargadi ‘yan Najeriya da kada su ruɗu da abin da ya kira “kyautar Girkawa”, yana mai cewa rage farashin da bai dawwama ba na iya jefa tattalin arziki cikin matsala a gaba.
Ya ce:
“Za ku iya jin daɗin farashi mara daidaito na ɗan lokaci, amma me zai faru nan gaba? ‘Yan Najeriya ne za su sha wahala.”
A ƙarshe, ya buƙaci duk masu ruwa da tsaki da su guji dabarun kasuwa na ɗan lokaci da ba sa amfanar ƙasa a dogon lokaci.
