Rasha ta kafe cewa ba ta shirin afka wa Ukraine

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergie Lavrov ya kafe cewa ƙasarsa ba ta son yin yaƙi da Ukraine, amma ya ce hakan ba yana nufin za su bari a yi musu yadda ake so ba.

Mista Lavrov ya ƙara da cewa bukatun da Amurka ta gabatar abin dubawa ne, kuma Shugaba Vladmir Putin na nazarin yadda zai mayar da martani. 

Sai dai jekadan Amurka a Moscow, John Sullivan, ya ce Rasha ce ke son kunna wutar rikici la’akari da yadda ta jibge sojoji a kan iyakarta da Ukraine.

Shi ma Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi ganawar fiye da awa ɗaya da Mista Putin kan batun, amma kawo yanzu ba a fitar da bayanai kan me suka tattauna ba. Kazalika, Macron zai tattauna da Shugaban Ukraine nan gaba kadan.

Lamarin ya fusata al’umma da ke zaune cikin zaman dardar, ganin cewa yaki na iya barkewa kowane lokaci. 

“Ya kamata a fahimci cewa Kasarmu kasa ce mai cikakken ‘yanci kuma idan ma adalci za a yi mana sai a bar mu mu zabi bangaren da muke so,” a cewar wata ‘yar Ukraine.