Rasha ta ce za ta mayar wa Amurka martanin soji kan Ukraine 

Rasha ta yi barazanar mayar da martanin da ta kira na dabarun soji idan Amurka ba ta biya mata bukatunta na tsaro ba, wadanda suka hada da janyewar dukkanin dakarun Amurkar daga gabashi da tsakiyar Turai.

Gargadin na a matsayin martini ne ga wata wasika ta Amurka wadda a ciki Amurkar ta yi watsi da kiran da Rasha ta yi da a ba ta tabbacin cewa ba za a taba bari Ukraine ta zama mamba a kungiyar tsaro ta Nato ba.

Haka kuma Rashar ta gaya wa kasashen Yamma da su daina tura makamai zuwa Ukraine sannan a janye masu bayar da shawara da bayar da horo na Yamma daga Ukraine din.

Can a Washington, Shugaba Biden ya ce barazanar Rasha ta mamayar Ukraine har yanzu tana nan sosai, kuma za ta iya kasancewa cikin ‘yan kwanaki – amma dai har yanzu yana da kwarin guiwar sasanta rikicin ta hanyar diflomasiyya.

A yau Rashar ta kori mataimakin jakadan Amurka daga Moscow Bart Gorman, abin da Amurkar ta ce ya saba hankali, kuma za ta mayar da martani a kai.