Rasha da Ukraine sun cimma yarjejeniyar fitar da cimakar da ke jibge a Ukraine zuwa kasashen ketare.
Shugaban Turkiya Raceip Erdogan ne tare da hadin gwiwa da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress suka shiga tsakani don cimma wannan yarjejeniyar tsakanin kasashe biyu da ke ci gaba da gwabza yaki,wanda hakan ke nufin cire nakiyoyin da aka daddasa a hanyar jigilar cimaka daga Ukraine da ke kan tekun Baharul Aswad ,lamarin da zai dawo da Ukraine cikin tsarin samar da abinci na duniya nan take, gami da abinci da takin da Rasha ke samarwa, zuwakasuwannin duniya.Shugaban na Turkiya dai Recep Tayyip Erdogan,ya siffanta yarjejeniyar da wani albushir ga kasashen duniya, kuma ministan tsaronsa,Halusi Akar ya sha alwashin ganin an aiwatar da yarjejeniyar sau da kafa.
Cika alkawari na tabbatar da yarjejeniyar da aka cimma.
“Wannan yarjejeniyar ta shafi bangarori da dama da suka hada da samar da kayyakin gudanarwar da suka wajaba don dakwan wannan cimakar cikin yanayin tsaron da ya wajaba.Turkiyya a shirye take ta ga ta aiwatar da wannan yarjejeniyar yadda ya kamata. Abun farin ciki shi ne,dukkanin bangarorin sun zaku don gani an fara aiwatar da wannan yarjejeniyar da za ta fitar da duniya daga ja,ibar karancin abinci.” Babban sakataren MDD Antonio Guterres,wanda ya yi kira da a dauki managartan matakai na zahiri don magance matsalar karancin abinci da ake fama da ita a duniya, ya yi fatar wannan yarjejeniyar ta zama danba na kawo karshen matsalar. To sai dai kamar yadda kakakin gwamnatin Ukraine,Mikhaeil Vodoliayak ya shaida ya kuma wallafa a shafinsa na Tweeter,kasar ta Ukraine ta cimma wannan yarjejeniyar da kasar Turkiya ne kadai da MDD,babu wata yarjejeniyar aiki tare tsakaninta da Rasha da ke kai mata hare-haren cin zalin da take shirin daukar fansa. Itama a nata bangaren,Amurka da ta yi maraba da rattaba hannu kan yarjejeniyar,ta ce a ta bakin kakakin sakataren harkokin wajenta,Ned Price ba a nan Gizo ke sakar ba.
Fitar da cimakar zai sa a samu faduwar frashin kayan abinci a duniya
“Muna maraba da shelanta wannan yarjejeniyar,sai dai abun da mu ka fi bai wa mahimmanci shi ne ,muna fata,Rasha za ta aiwatar da wannan yarjejeniyar ba da wata kunbiya-kunbiya ba,don a samu a isar da wannan cimakar zuwa ga kasuwannin duniya.” Kimanin tan miliyan 22 ne dai ke jibge a kasar ta Ukraine da ake jiran fitar da shi,lamarin da ake sa ran idan har ya tabbata,zai taka birki a hauhawan farashin cimaka a duniya,koma ya kawo faduwarsa.