PTAN Ta Roki Gwamnatin Tarayya akan Jihohi Da Su Sanya Jami’an Tsaro A Makarantu
Shugaban kungiyar iyayen yara ta kasa (PTAN), Alhaji Haruna Danjuma, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su samar da isassun jami’an tsaro a dukkan makarantu domin dakile hare-haren ‘yan bindiga yayin da aka sake bude makarantu a yau.
A wata sanarwa da ya fitar a Kaduna ranar Lahadi, Danjuma ya ce hakan zai kara wa iyaye kwarin gwiwar mayar da ‘ya’yansu makaranta.
“Muna rokon daukacin jihohin Najeriya 36 da gwamnatin tarayya da su taimaka mana da kare ‘ya’yanmu ta hanyar samar da isassun jami’an tsaro a harabar makarantar,” inji shi.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su koma kan teburin tattaunawa domin kawo karshen yajin aikin na watanni shida.
Ya kuma tunatar da gwamnatin jihar Kebbi da gwamnatin tarayya da su rubanya kokarin ganin an ceto sauran dalibai mata 11 da aka yi garkuwa da su na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin-Yauri.
Ya koka da yadda har yanzu ‘yan matan Yawuri na hannunsu bayan kwanaki 445 kuma babu wanda ya ke magana a kai.
Hakazalika, wata gamayyar matan arewa ta yabawa rundunar sojojin Najeriya, FG, da kuma ‘yan banga bisa nasarar fatattakar ‘yan bindiga da maboyar ‘yan ta’adda a dajin Kaduna.
Shugabar kungiyar kare hakkin mata da yara ta kasa a Najeriya, Hajiya Ramatu Tijjani, ta ce hare-haren da sojoji ke kai wa a dajin Kaduna ya gurgunta ayyukan ‘yan bindiga.