NLC Ta fara  Zanga-zanga Akan Wahalhalun Rayuwa

NLC Ta fara Zanga-zanga Akan Wahalhalun Rayuwa

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta fara zanga-zangar adawa kan wahalhalun da ake fama da su a fadin kasar duk kuwa da kokarin da gwamnatin tarayya ta yi na hana hakan.

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya gayyaci shugabannin kungiyar kwadago zuwa ofishin sa.

A karshen taron, Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ya ce duk da tsoma bakin da aka yi na dakile zanga-zangar a fadin kasar, za ta ci gaba da tafiya kamar yadda aka tsara.

Sai dai ya bukaci jami’an tsaro da su kare masu zanga-zangar.