Nijar: Kin amincewa da sojojin Faransa
Kawancen kungiyoyin fafutika na Nijar na M62 ya sha alwashin bijire wa karbar sojojin Faransa da kasar ta yi bayan ficewar da suka yi daga Mali. Wannan na zuwa ne duk da haramcin zanga-zanga da mahukunta a Yamai suka yi.
Jaridar DW ta wallafa cewa, A ranar Litinin ne dai ayarin karshe na motoci kimanin 50 na rundunar sojoji ta Barkhane ta sojin Faransa a Mali ya ketaro zuwa cikin kasar Nijar bayan ficewa daga kasar ta Mali. A yanzu sojojin Faransan za su girke hedikwatarsu a cikin kasar ta Nijar domin ci gaba da yaki da ta’addanci. Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar, kawancen kungiyoyin farar hula na M62 mai adawa da girke sojojin ketare musamman na Faransa a Nijar, ya yi tir da zuwan sojojin Faransar tare da shan alwashin ci gaba da yakar zamansu a kasar. Sai dai kuma a daidai loakcin da kawancen kungiyoyin na M62 ke tir da Allah wadai da zuwan sojojin rundunar ta Barkhane a Nijar, wasu kungiyoyin farar hula lale marhabin suka yi da zuwan nasu. Malam Lawal Tsaiyyabou shi ne shugaban kawancen kungiyoyin farar hula na RODDAD, ya kuma ce duk mai hankali ya san zaman sojojin ya dace. To amma duk da haka, kawancen na M62 ya tsara shirya zanga-zanga a ranar Laraba a birnin Yamai. Zanga-zangar da mahukuntan birnin Yamai suka ce sun haramta.