“Ni dai na fara ina fatan za’a biyo ni” : Ali Rabi’u Ali Daddy

Shahararren Danwasan Hausa Ali Rabi’u Ali wanda aka fi sani da DADDY, Ya bayyana a shafinsa na Facebook wani sabon shirin film din da ya zo meuk da shi a wannan shekarar me Zuwa ta 2022

“BAWAN ALLAH! sabon shiri na Hausa mai dogon zango akan tarbiyyar Addinin Musulunci. Wannan shi ne burina tun fara harkar fina finan Hausa a shekara ta 1999, amma na rasa goyon bayan wadanda za mu yi wannan aikin alkhairin, idan na yunkuro sai a dankwafe ni, in tashi da kyar saboda mafiya yawan mutane sun shagala da fina finan nishadi kawai. Amma yanzu cikin yardar Allah na yi damara kuma na saka danba zan fara sakinsa a farkon shekarar 2022 a tasha ta ta YouTube mai suna ALI DADDY HAUSA TV

Ina Neman gudunmowar Ku masu kishin Addinin Musulunci kar Ku bari wannan aiki ya tsaya domin amfanin addini mu. Bangaren Addu’a da bibiya da kuma shawarar masana masu ilimi yadda zamu yi shirin da zai amfanar ba tare da kawo sabani ko bambancin ra’ayi a Musulunci ba. Yadda za mu karu da Ilimi na rayuwa da zamantakewa da shugabanci na Gida da na al’umma bisa tarbiyyar Addinin Musulunci. Inda na yi kuskure Allah Ya yafe min inda na kwatanta Allah Ya tsarkake min zuciyata ga barin yin riya.

Fatana kannywood gaba daya ta koma yin fina finai akan doron shari’ar Musulunci. Ni dai na fara ina fatan za’a biyo ni”.