Neymar zai fuskanci shari’a kan badakalar cinikin ‘yan wasa

Neymar da Silva Santos Junior, wanda aka fi sani da Neymar, zai gurfana a gaban kotu a watan Oktoba, bisa zarginsa da aikata ba daidai ba wajen komawarsa Barcelona, ​​in ji majiyoyin shari’a a ranar Laraba.

Za a gurfanar da dan wasan na Brazil, iyayensa, da tsoffin shugabannin Barcelona Sandro Rosell da Josep Maria Bartomeu bisa zargin cin hanci da rashawa da suka shafi tafiyar dan wasan gaba daga Santos zuwa Barcelona a 2013.

Rosell da Bartomeu kuma za su fuskanci tuhume-tuhumen damfara a shari’ar da aka shirya yi daga ranar 17 zuwa 31 ga watan Oktoba.

Neymar ya bar Barcelona zuwa Paris Saint-Germain a shekara ta 2017 kan kudi Euro miliyan 222 a tarihin duniya, sai dai komawarsa daga kulob din Santos na matashi zuwa Barca wanda ya haifar da cece-kuce.

Lamarin ya samo asali ne daga korafin da kungiyar DIS ta Brazil, tsohon mai kaso na hakkin dan wasan ya yi.

A hukumance Barcelona ta ce cinikin ya ci Yuro miliyan 57.1 (dala miliyan 63.6), tare da Euro miliyan 40 ga dangin Neymar da kuma miliyan 17.1 ga Santos, amma daga baya masu gabatar da kara na Spain sun ce a zahiri ya ci akalla Yuro miliyan 83.3.

Hukumar ta DIS, ta karbi miliyan 6.8 daga cikin Yuro miliyan 17.1 da aka biya wa Santos, ta yi zargin cewa Barca da Neymar sun hada karfi da karfe wajen boye hakikanin adadin kudin da aka sayo.

Masu gabatar da kara sun bukaci da a yankewa Neymar hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari, amma ya dage cewa ya mayar da hankali ne kawai a fagen kwallon kafa, kuma a makance ya aminta da mahaifinsa, wanda kuma shi ne wakilinsa.