NEMAN SAFARA’U DA MR 442 MUKE RUWA A JALLO

Shugaban Hukumar Tace Finafinai Na Jihar Kano Isma’ila Afakallahu A wata tattaunawa da shugaban hukumar tace finafinai na jihar Kano, Isma’il Na’abba Afakallu ya yi da jaridar SARAUNIYA NEWS ta bayyana cewar, yanzu haka neman Safara’u suke yi ruwa a jallo ita da mawaƙi Mr 442.

Ya ƙara da cewa yanzu haka sun arce sun yi ƙaura daga jihar Kano, domin dokar jihar ba zata ba su damar yin abinda suke so na ɓata tarbiyya ba.

Haka bazai rasa nasaba ba da Yadda mawakiyar ta tsefe idanuwanta a cikin Al’umma wajen aiwatar da wakokin su tare da 442 ba tare da kunyar Jama’a ba,

Musamman idan ka shiga shafukan sada zumunta musamman shafin nan na Tiktok Inda basa kunayar Furta kalmomin batsa a wakokin su da kuma abubuwan da suka sabawa Addini da al’adarsu.