Nato za ta fara atisayen gwajin ƙarfinta
Ƙungiyar tsaron NATO za ta fara wani atisayen gwajin ƙarfin da take da shi na kare kanta daga abokan gaba.
Ta kira gwajin wanda za ta yi a yankin Baltic da suna Hedgehog, wanda zai kunshi kasashe 10, ciki hadda kasashen Finland da Sweden da ake saran su kammala shigarsu ƙungiyar a cikin makon nan.
Dama an shirya atisayen tun kafin kutsen Rasha a Ukraine, amma a yanzu zai zama wata manuniya kan gano karfin da kasashen Baltic suke dashi na kare kansu daga irin wannan kutse.
Firanministar Sweden Magdalena Andersson na shirin jagorantar wani zama kan shirin kasar na kammala zama mamba a NATO, kuma can ma a Finland za a yi irin wannan tattaunawa.