Najeriya ta roki China ta taimaka wajen kubutar da fasinjojin jirgin kasar da aka sace
Kwamitin kula da harkokin sufuri a majalisar wakilan Najeriya, ya roki gwamnatin China da ta taimaka wajen ganin an kubutar da fasinjojin jirgin kasan nan 62 da aka sace a ranar 28 ga watan Maris a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja.
Shugaban kwamitin Sanata Abdulfatai Buhari, wanda ya yi magana a madadin ‘yan kwamitin a yayin wata ziyarar gani da ido da kwamitin ya kai tashar jirgin kasa ta Obafemi Awolowo da ke Ibadan ya bayyana rashin jin dadinsa a kan rashin kubutar da mutanen har kawo yanzu.
Sanatan ya ce harin da aka kai kan jirgin kasan ya sanya fargaba a zukatan ‘yan Najeriya wadanda suka koma tafiye-tafiye ta jirgin.
Ya ce, ba laifi ba ne idan gwamnatin China ta zo ta taimaka wa Najeriya wajen ceto fasinjojin.
Kamfanin kasar China ne dai ya gina layin dogon da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna wanda ke da nisan kilomita 159.
Sanatan ya ce, gwamnatin China ta samu kudi daga irin ayyukan da kamfaninta na CCECC ya yi a Najeriya, don haka ba gazawa ba ce idan an nemi su zo su taimaka.